Ka Yafe Wa Igbobo, Ya Wahala, Ya Gane Kurensa: Basaraken Yarbawa Ya Roƙi Buhari

Ka Yafe Wa Igbobo, Ya Wahala, Ya Gane Kurensa: Basaraken Yarbawa Ya Roƙi Buhari

  • Oba Abdulrasheed Akanbi, Oluwa na Iwo, ya rubuta wasika ga Shugaba Buhari don nema wa Sunday Igboho afuwa
  • Basaraken na Yarbawa ya ce Sunday Igboho dansu ne amma akwai kuruciya da kuskure cikin hanyar da ya ke gudanar da gwaggwarmayarsa
  • Oba Abdulrasheed Akanbi ya ce Igboho ya sha wahala sannan ya gane kurensa kuma ya yi alkawarin zai mika shi ga idan har an masa afuwa

Oluwa na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Igboho afuwa, Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa jami'an hukumar yan sandan farar hula DSS sun kai samame a gidansa da ke Ibadan a makon da ta gabata inda aka kashe mutum biyu.

Ka yiwa Igboho afuwa, zan kawo shi tattauwar zaman lafiya, Sarkin Yarbawa ya roki Buhari
Ka yiwa Igboho afuwa, zan kawo shi tattauwar zaman lafiya, Sarkin Yarbawa ya roki Buhari. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

Kara karanta wannan

Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari

DSS ta yi holen mutanen da ta kama a gidansa da makamai da wasu kayayyaki da aka samu, Igboho ya samu ya tsere a yayin da mutanensa ke musayar wuta da jamian DSS yayin samamen.

Nan take aka ayyana nemansa ruwa a jallo aka shawarci ya mika kansa domin babu inda zai boye.

A martaninsa, Oluwo, cikin wasikar da ya rubuta game da lamarin Igboho ya shawarci Shugaban Kasa ya sassauta farautar da ya ke yi wa Igboho.

KU KARANTA: Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

The Punch ta ruwaito cewa wani sashi na wasikar ya ce:

"Sunday Igboho ya yi fice ne a matsayin dan gwagwarmaya da ke son kwato hakkin wadand ake zalunta. Ban san tsarinsa ba saboda ba tare muke aiki ba. Duk lokacin da na samu bayani game da abin da ya ke yi, na kan kira shi in bashi shawara.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bayyana adadin mutanen da aka kashe daga shekarar 2011 zuwa 2021

"Igboho ya kasa gane banbanci tsakanin gwagwarmaya ta gwamnati da gwagwarmaya tsakanin kungiyoyi. A wani lokacin ya zagi masu ruwa da tsaki. Ina cikin mutanen farko da suke kira ga Nigeria daya. A matsayina na mahaifi, na yafe masa. Ina rokonka a matsayin shugaban Nigeria ka yafe wa danmu Chief Adeyemo Sunday Igboho.
"Dan koyo ne a harkar gwamnati. Ya yi alkawarin zai saurare mu. Ina rokon mai girma shugaban kasa ya sasauta farautar da ya ke yi wa Igboho. Ina fatan wannan rubutun zai karfafa zaman hadin kan Nigeria. Ina yi wa mai girma shugaban kasa alkawari daga yanzu Igboho zai fara takatsantsan. Ya sha wahala sosai. Zai sasauta fafutikarsa. Zan kawo shi domin tattaunawar zaman lafiya a lokacin da ya dace."

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Matasan Tibi Sun Yabawa Buhari Kan ‘Ragargazan’ Nnamdi Kanu da Sunday Igboho

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel