WhatsApp Zai Fara Karbar Kudin Tura Sakonni daga hannun 'Yan Najeriya
- Meta za ta fara cazar 'yan Najeriya kudin sakonnin WhatsApp daga ranar 1 ga Okutoba, 2026 kamar yadda aka sanar
- Sauyin zai shafi kamfanonin da ke amfani da WhatsApp Business Platform wajen magana da kwastomomi
- Kanana da matsakaitan sana’o’i (SME) da kamfanonin sadarwa na zamani za su iya sauya tsarin tafiyar da harkokinsu saboda karin kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Masu sana'o'i a Najeriya da suka dogara da WhatsApp wajen magana da kwastomominsu za su fuskanci batun sabon tsarin kudin gudanar da sana'a a manhajar.
Hakan na zuwa ne yayin da kamfanin Meta mamallakin WhatsApp da Facebook yake shirin fito da tsarin cazar kudi kan wasu sakonnin kasuwanci daga ranar 1 ga Okutoba, 2026.
Wannan sauyi zai iya haifar da tsaiko ga kamfanonin da 'yan kasuwa da ke amfani da manhajar a gaba daya wajen hulda da kwastomomi, tallace-tallace, da aika sakonnin kudi.
Sauran ayyukan da abin zai shafa sun hada da tabbatar da odar kaya da sauran muhimman sakonnin yau da kullum da masu kasuwanci ke aikewa.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Saudi Arabia ta kafa sabbin ka'idojin daukar ma'aikata 'yan kasashen waje

Source: Facebook
WhatsApp Business zai fuskanci sabon tarnaƙi
Karkashin sabon tsarin farashin, kamfanoni ko da kasuwan da ke amfani da WhatsApp Business Platform za su rika biyan kudi kan sakonnin da aka tura musu.
Irin wadannan sakonnin na daga cikin waɗanda a baya ake aikawa kyauta karkashin tsarin taimakawa kwastomomi na tsawon sa'o'i 24.
A gefe guda, wannan sauyi ba ya nufin cewa sauran mutane da ke amfani da WhatsApp za su fara biyan kudin tura sakonsu.
Haka zalika, kamfanonin da ke amfani da tsarin WhatsApp Business gama gari ba su ne kan gaba wajen fuskantar wadannan biyan kudaden ba.
Wadanda abin ya fi shafa su ne kamfanonin da suka dogara da Business Platform na Meta wajen gudanar da harkokinsu da mutane da dama.
Nawa ne kamfanonin Najeriya za su rika biya?
A bangaren kamfanonin Najeriya, kudin da za su yi za ta kashewa ya dogara ne kan nau’i da kuma adadin sakonnin da suka tura.

Kara karanta wannan
Dama ta samu: Kamfani ya ware Naira biliyan 20 domin tallafa wa matasa yan kasuwa a Najeriya
Sakon da aka tura zuwa lambar Najeriya zai kusa kai $0.0101, wanda ya yi daidai da kusan N14 kamar yadda kamfanin na Meta ya bayyana.
Sakonnin tallace-tallace za su fi tsada sosai, inda sakonsu zai kai kusan $0.062, wanda ya kai kusan N84 a kowane sako guda.
Duk da cewa kudin sako guda zai iya zama kadan a idon mutane, kudaden za su yi yawa idan aka tura dubban sakanni ko miliyoyi.
Misali, kamfanin hada-hadar kudi na Najeriya da ke aika sakanni 500,000 kan $0.0101 zai iya fuskantar cajin $5,050 daga wurin Meta.
Akwai kuma karin kudaden da sauran kamfanonin samar da tsare-tsaren kwamfuta za su iya dorawa kan kudin gaba daya.
SME, bankuna da kamfanonin fintech za su fuskanci kalubale
Wannan abu yana da matukar muhimmanci a Najeriya, inda WhatsApp ya zama babbar hanyar gudanar da harkokin kasuwanci.
Bankuna da kamfanonin hada-hadar kudi da aka fi sani da fintech suna amfani da dandalin wajen magana da kwastomomi, yayin da 'yan kasuwa suka dogara da shi wajen karbar oda.
Kamfanonin jiragen sama, kamfanonin sadarwa da sauran masu hada-hadar kasuwanci a yau da kullum su ma suna amfani da manhajar wajen sarrafa bukatun mutane.

Kara karanta wannan
N700,000 don samun mace? Babban malami ya ƙaddamar da shafin haɗa aure a Najeriya
A bangaren kananan sana'o'i, sabbin kudaden za su iya tursasa musu sake tsara yadda suke amfani da dandalin kasuwancin na WhatsApp.
Wannan zai shafi wadanda ke amfani da WhatsApp a matsayin hanyar tallata kaya da taimakawa kwastomomi, kamar yadda rahoton Daily Sun ya bayyana.
Wajibi ne kamfanoni su rika tantance muhimman sakonni, rage hanyoyin magana marasa amfani, da kuma lura da kudin da suke kashewa.
Meta na fadada hanyoyin samun kudin shiga a WhatsApp
Kamfanin Meta yana tafiya tsarin cazar kudi kan kowane sako tun daga watan Yulin 2025, inda ya sauya tsarin cazar kudi na baya da kowa ya saba da shi.
Sauyin na watan Okutoban 2026 zai tsananta ne ta hanyar cire damar samun damar hulda kyauta a tsawon sa'o'i 24 na fara taimakawa kwastomomi.
Ga kamfanonin Najeriya da suka gina hanyoyin magana da kwastomominsu a WhatsApp, sakon a fili yake cewa dandalin ya daina zama kyauta na kyauta gare su.
Wanda ya tantance Salisu Ibrahim, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng