"Babu Sulhu": Gwamna Dauda Ya Fadi Shirinsa kan Kawo Karshen 'Yan Bindiga

"Babu Sulhu": Gwamna Dauda Ya Fadi Shirinsa kan Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake taso da batun yin sulhu da 'yan bindiga masu kai hare-hare
  • Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu da 'yan bindiga ba wadanda suka addabi mutane a jihar Zamfara
  • Gwamnan ya bayyana cewa zai ci gaba da yi tsayin daka wajen hadaka da hukumomin tsaro domin ganin an murkushe 'yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin sulhu da ‘yan bindiga.

Gwamna Dauda ya ce a maimakon yin sulhu, gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da matakan soja kan 'yan bindiga har sai sun mika wuya ko kuma doka ta yi aiki a kansu.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna kuma tsohon kwamishina a Bauchi ya riga mu gidan gaskiya

Gwamna Dauda Lawal ya ce ba zai yi sulhu da 'yan bindiga ba
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, na jawabi a wajen taro Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Mukhtar Musa, yayin kaddamar da sakatariyar kungiyar 'yan asalin jihar Zamfara mazauna Kaduna a ranar Lahadi, 5 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton Vanguard.

Haka zalika, taron ya hada da rabon kayan abinci ga mambobin kungiyar marasa galihu da ke Kaduna.

Wace hanya Gwamna Dauda zai bi?

Mukhtar Musa ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal ta tsaya tsayin daka wajen kawo karshen rashin tsaro ta hanyar ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin tsaro a fadin jihar.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da samar da ababen hawa, kayan aiki, alburusai da sauran tallafin aiki ga dakarun tsaro da ke yaki da miyagu.

“Gwamna ba zai taba yin sulhu da ‘yan bindiga ba. Wadanda ke son mika wuya su yi hakan ko kuma su fuskanci doka."

- Gwamna Dauda Lawal

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan bindigan har sai an dawo da zaman lafiya mai dorewa a fadin Zamfara.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Ƴaƴan tsohon mataimakin gwamnan Bauchi sun rasu a hatsarin mota

Hanyar da jama'a za su taimaka a yaki 'yan bindiga

Mukhtar Musa ya bayyana cewa bayanan sirri daga mazauna jihar na da matukar muhimmanci wajen samun nasara a yakin da ake yi da rashin tsaro.

Ya bukaci mutane da su gaggauta kai rahoton duk wani motsi ko ayyuka na zargi ga hukumomin tsaro domin daukar mataki cikin gaggawa.

Gwamna Dauda ba zai yi sulhu da 'yan bindiga ba
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Hakazalika, ya tabbatar wa mambobin kungiyar cewa gwamnan ya jajirce wajen kawo ci gaba mai ma'ana da kuma dawo da zaman lafiya a fadin Zamfara.

Mukhtar Musa ya bayyana taron a matsayin mai muhimmanci, inda ya ce yana nuna hadin kai tsakanin 'yan asalin jihar Zamfara da ke zaune a wajen jiharsu ta haihuwa.

Ya yaba wa wadanda suka shirya taron bisa nasarar kafa sakatariyar kungiyar ta jiha a Kaduna, jaridar The Punch ta kawo labarin.

'Yan bindiga sun kashe babban limami

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Umarnin da fadar shugaban kasa ta ba DSS, EFCC kan batun ma'aikatar bogi

'Yan bindiga dauke da makamai sun kashe babban limamin kauyen Talluje da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto

Hatsabiban sun kai harin ne a Talluje da kuma kauyen Chofi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane biyu tare da tilasta wa daruruwan mutane guduwa daga gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng