'Ƴan Bautar Ƙasa Sun Fi Mu Albashi': Lakcarori a Babbar Makaranta Sun Koka a Kaduna
- Kungiyar ASUP a Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli ta ce malamanta na karɓar albashi ƙasa da na NYSC, lamarin da ke haddasa ficewar ƙwararru
- Shugaban ASUP Usman-Shehu Suleiman ya bayyana yawan albashin malami mai matsayi mafi ƙasa yake karba a wata
- Kungiyar ta zargi gwamnati da saba alkawura tun 2009, inda har yanzu ba a aiwatar da tsarin sabon albashi da aka ɗauka ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Kungiyar malamai a Kwalejin Fasaha a jihar Kaduna ta yi korafi kan karancin albashi.
Kungiyar ASUP reshen Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli a Zaria ta nuna damuwa kan albashin da malamanta ke karɓa.

Asali: Facebook
Nuhu Bamalli: Malamai sun koka kan albashi
Shugaban kungiyar, Usman-Shehu Suleiman, ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi suka ce kungiyar ta ce hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da yajin aikin a Kwalejin a halin yanzu.
Kungiyar ta zargi cewa albashin malamai bai kai na matasa masu bautar ƙasa ta hukumar NYSC ba.
Sanarwar ta ce lamarin na kara tayar da hankula kan halin da malamai suka tsinci kansu a ciki.
Malaman Kwaleji sun shiga yajin aiki a Kaduna
An ruwaito cewa hadakar ƙungiyoyin ma’aikatan sun fara yajin aikin gargadi na mako guda ranar 16 ga Yuni, wanda ya dakatar da karatu a makarantar.
Yajin aikin na da nasaba da rashin aiwatar da tsarin albashi na Kwalejojin Ilimi da Fasaha da batun ritaya a shekara 65.
Suleiman ya ce albashin mataimakin lakcara a Kwalejin bai wuce N64,400 ba a wata.
Ya ce:
“Wannan, da sauran matsaloli, na haddasa yawaitar barin aiki daga malamai, inda da dama ke komawa jami’o’i da sauran makarantu a ƙasar nan.
“Mun rasa malamai da dama da suka koma jami'ar sufuri da ke Daura, Kwalejin Fasaha ta Tarayya a Gombe da jami'ar jihar Kaduna.
“Wani malami da aka ɗauki nauyin karatunsa na 'Masters' da Ph.D ya dawo sai ya fice saboda yanayin bai masa ba."

Asali: Original
Yadda malamai ke gwagwarmaya da gwamnati
Sai dai shugaban ya ce malamin ya rattaba hannu kan yarjejeniya da makaranta, wanda hakan ya sa dole ya biya fiye da N21m.
Shugaban ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “hatsari” ga tsarin ilimi a jihar da ƙasa baki ɗaya, Daily Post ta ruwaito.
Haka kuma, Abubakar Aliyu-Shika, shugaban SSANIP reshen makarantar, ya ce suna fafutukar sabon albashi tun 2009 har zuwa yanzu.
Kano: Gobara ta yi barna a kwalejin fasaha
Kun ji cewa mummunar gobara ta tashi a kwalejin fasaha ta jihar Kano, inda ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa.
An ruwaito cewa gobarar ta babbake kafatanin sashen koyon 'Arts and Industrial' na bangaren da ke a bangaren koyon fasaha na kwalejin.
Kakakin hukumar kashe gobara na Kano, Saminu Abdullahi wanda ya tabbatar da lamarin ya ce har yanzu ba a gano musabbabin wutar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng