Tinubu zai Dauki Matasa 5,000 domin ba Su Horo Su Samu Sana'a

Tinubu zai Dauki Matasa 5,000 domin ba Su Horo Su Samu Sana'a

  • Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin horas da matasa 5,000 a matsayin masu sanya mita a gidaje da wuraren aiki
  • An bayyana cewa shirin shafi matasan da suka kammala sakandare, tare da ware gurbi na musamman ga masu yi wa ƙasa hidima
  • Gwamnatin Najeriya ta ce hakan na da burin ta na rage ƙarancin mita, kawo ƙarshen rashin tsari wajen kuɗin wutar lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da ƙaddamar da wani shirin horas da matasa 'yan Najeriya 5,000 a matsayin masu sanya mita da ƙwararrun masu aikin mita ƙarƙashin shirin PMI.

Tinubu ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin samar da ayyukan yi, rage ƙarancin mita a faɗin ƙasar da kuma inganta samar da wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Tinubu ya kaddamar da sabon shiri da matasa 5000 za su samu aiki

Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu, mitar wutar lantarki a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce shirin na daga cikin ajandar gwamnatinsa domin faɗaɗa damar aikin yi ga matasa.

Horon da za a ba matasa 5,000

A cewarsa, shirin zai ba mahalarta horo na ƙwarewar fasaha tare da haɗa su da damar samun aikin yi a fannin wutar lantarki a Najeriya.

"Mun buɗe wata sabuwar dama ga matasa 'yan Najeriya 5,000 domin a horas da su a matsayin masu sanya mita da ƙwararrun masu aikin mita.
"Wannan shiri ya shafi ayyukan yi da ƙwarewa,"

In ji shi.

Matasan da za su amfana

Punch ta wallafa cewa Tinubu ya ce shirin zai kasance a buɗe ga 'yan Najeriya da suka kammala karatun sakandare, tare da ware gurbi na musamman ga masu yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Ya bayyana cewa faɗaɗa amfani da mitar lantarki yana da matuƙar muhimmanci wajen inganta ayyukan wutar lantarki da kuma ƙara gaskiya a fannin.

Kara karanta wannan

Zabe na karatowa, Tinubu zai ciwo bashin dala biliyan 1.25 a bankin duniya

Ya ce idan gidaje da wuraren kasuwanci suna da mita yadda ya kamata, mutane za su biya kuɗin wutar da suka yi amfani da ita kawai.

Haka kuma, kamfanonin rarraba wutar lantarki za su riƙa tara kuɗin shiga cikin gaskiya, abin da zai taimaka wajen rage asara, kula da kayan aiki da inganta ayyuka.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaban ya ce ya umarci masu kula da PMI su haɗa kai da ma'aikatar bunƙasa matasa ta tarayya, cibiyar horar da ma'aikatan wutar lantarki ta kasa (NAPTIN) da sauran masu ruwa da tsaki domin fara shirin cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Ya kuma ƙarfafa matasan da suka cancanta su nemi shiga shirin, yana mai cewa zai ba su ƙwarewar da za ta samar musu da abin dogara da kansu.

Tinubu ya kaddamar da titi

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da titin Jos/Akwanga da zai ratsa wasu jihohin Arewa.

Shugaban kasar ya bayyana cewa aikin titin zai samar da ayyukan yi tare da hada kan al'umma a jihohi biyar da zai ratsa a Arewacin Najeriya.

Shugaban jam'iyyar APC da ya wakilci shugaba Bola Tinubu a wajen kaddamar da aiki ya samu rakiyar gwamnoni da wasu shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng