Bayan Barazanar Trump, Iran na Neman Karamin Dansa, Ta Sanya Tukucin $10m
- Wasu rahotanni daga Iran ya watsa wani bidiyo da ke nuna ana bibiyar Barron Trump domin samun bayanai kansa
- Bidiyon ya bayyana wurin jami’ar Barron, motocin rakiyarsa da jami’an tsaro, tare da cewa an gano hanyoyin sadarwarsa
- Wannan barazana ta biyo bayan wasu bidiyoyi da kafafen yaɗa labaran Iran suka fitar kan Donald Trump da Melania Trump
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Wasu rahotanni daga gwamnatin Iran sun watsa wani bidiyo da ake ikirarin yana bibiyar ɗan ƙaramin ɗan Shugaban Amurka Donald Trump.
An ce ana bibiyar Barron Trump, tare da nuna wurin da yake zama, motocin rakiyarsa da wuraren da jami’an tsaronsa na farin kaya suke.

Source: UGC
Ladan da Iran ta saka kan yaron Trump
An yada wani bidiyo da ake ikirarin yana nuna yadda ake bibiyar Barron Trump, ɗan Donald Trump mai shekaru 20, tare da cewa an sanya ladan dala miliyan 10 kan duk wanda ya taimaka wajen kashe shi, cewar Euronews.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Bidiyon ya yi ikirarin nuna wurin da jami’ar Barron take, motocin da ke yi masa rakiya da kuma wuraren da jami’an farin kaya ke tsaye, yana cewa an “sa ido sosai” kan zirga-zirgarsa.
Sai dai, ba a iya tabbatar da sahihancin ikirarin cewa an sanya ladan dala miliyan 10 kan Barron Trump ba a lokacin da aka wallafa rahoton.
Bidiyon ya kuma yi ikirarin cewa wata “yarinya” ta samu hanyar wuce kariyar jami’an tsaron farin kaya ta zauna da Barron Trump a wani taro na sirri, sannan ta mika bayanai ga masu shirya shirin.
Haka kuma, bidiyon ya yi ikirarin cewa Barron Trump yana yin magana ta sirri ta murya da saƙonnin rubutu a Xbox, ba tare da jami’an tsaronsa suna kusa da shi ba.
Watsa wannan bidiyon ya biyo bayan wani makamancin sa da kafar yada labarai Tasnim, wadda ke da alaƙa da IRGC, ta fitar a watan Yuli mai taken.

Kara karanta wannan
Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027
Bidiyon na watan Yuli ya yi bayani kan zirga-zirgar Melania Trump a New York, tare da nuna wasu wuraren da ake zargin akwai rauni a tsarin tsaronta.
A ƙarshen watan Mayu, jaridar New York Post ta kuma ruwaito wani shiri da ake zargin an ƙulla domin kai hari kan Ivanka Trump.

Source: Getty Images
Trump na cikin barazanar Tehran
Kafofin yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun yi barazana kai tsaye ga Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya kara rikici tsakanin kasashen, cewar Punch.
A watan Yuli, wani allo mai ɗauke da hoton Donald Trump kamar gawa a cikin akwatin gawa ya bayyana a dandalin juyin juya halin Musulunci da ke Tehran, tare da rubutun “Za mu kashe Trump” da Turanci.
Wani bidiyo da aka fitar a baya ya kuma yi ƙoƙarin nuna hanyar da ayarin motocin Trump ke bi daga filayen jiragen sama zuwa gidajensa da ke Florida da New York.
UAE ta yanke alakar kasuwanci da Iran
An ji cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da duk wata huldar kasuwanci da Iran, sakamakon hare-haren da take zargin kasar.
Matakin ya zo ne bayan karewar yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, wadda aka tsara domin bude kawo karshen yakin.
Rahotanni sun ce Iran na nazarin wasu hanyoyin fadada yakin, ciki har da kai hari kan sansanonin Amurka.
Asali: Legit.ng
