Yadda aka Ce Iran Ta So Kustawa Gidan Netanyahu Ta Kashe Dan Shi
- Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce Iran ta yi yunkurin kashe daya daga cikin ’ya’yansa maza, sai dai bai bayyana wanda abin ya shafa ba
- Netanyahu ya ce wannan ne dalilin da ya sa ake ci gaba da bai wa ’ya’yansa da matarsa kariyar jami'an tsaro, yana mai cewa ba wata gata ba ce
- Rahotanni sun ce hukumomin tsaron Isra'ila sun san da zargin yunkurin tun watanni, amma babu cikakken bayani ko wata hujja mai zaman kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tel Aviv, Isra'ila – Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi ikirarin cewa Iran ta yi yunkurin kashe daya daga cikin ’ya’yansa maza.
Netanyahu ya yi wannan ikirari ne yayin wata hira ta wayar tarho da wasu 'yan jarida masu goyon bayan gwamnatinsa.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Source: Getty Images
Rahoton Roya News ya ce Netanyahu bai bayyana sunan dan nasa da ake zargin an yi wa yunkurin kisa ba, haka kuma bai yi karin bayani kan lokacin da abin ya faru ko yadda aka shirya yunkurin ba.
Batun kashe dan Netanyahu
Firaministan na Isra'ila ya ce barazanar da ake fuskanta ce ta sa ya goyi bayan ci gaba da bai wa iyalansa kariyar jami'an tsaro.
Ya ce:
“Iran ta yi wa daya daga cikin ’ya’yana barazana. Iran ta yi yunkurin kashe daya daga cikin ’ya’yana.”
Netanyahu ya ce kariyar da ake bai wa ’ya’yansa biyu, Yair da Avner, da kuma matarsa Sara, ba wata gata ba ce.
Ya bayyana cewa matakin kariyar zai iya ci gaba na akalla shekaru biyar, har ma idan ya bar mulki bayan zabe mai zuwa.
An ce akwai rahoton lamarin
Netanyahu bai bayyana ko Yair ko Avner ne aka yi wa yunkurin kisan ba, yayin da babu wata cikakkiyar hujja mai zaman kanta da aka bayyana a bainar jama'a domin tabbatar da ikirarinsa.
Sai dai wani rahoto daga Reuters ya ce yunkurin ya faru ne lokacin da daya daga cikin ’ya’yan Netanyahu yake wajen Isra'ila.
Rahoton ya kuma ce hukumomin tsaron Isra'ila sun san da batun tun watanni da suka gabata, amma an hana yada cikakkun bayanansa saboda dokar tace bayanan tsaro.
A cewar rahotanni, Yair Netanyahu, wanda aka san shi da tsattsauran ra'ayinsa kan harkokin siyasa, ya shafe lokaci mai tsawo yana zama a birnin Miami na Amurka, yayin da Avner ke zaune a Isra'ila.
Netanyahu ya nemi kariya
Maganar Netanyahu ta zo ne yayin da tsarin kariyar tsaron iyalansa ya zama batun muhawara a tsakanin ’yan siyasa da jama'a a Isra'ila.
Firaministan ya ce akwai bukatar ci gaba da bai wa iyalansa kariya saboda barazanar da ya ce suna fuskanta daga Iran.

Source: Getty Images
Sai dai har yanzu ba a samu cikakken bayani daga hukumomin Iran ko wata hujja mai zaman kanta da za ta tabbatar da cewa gwamnatin Tehran ce ke da hannu a yunkurin da Netanyahu ya bayyana.
Amurka za ta yaki tattalin Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump ta ƙaddamar da wani sabon shirin matsin tattalin arziki kan Iran.
Ministan Baitul Malin Amurka, Scott Bessent, ya ce manufar shirin ita ce katse dukkan hanyoyin samun kuɗin gwamnatin Iran da kuma matsa wa ƙasashe da kamfanonin da ke hulɗa da Tehran lamba.
Gwamnatin Donald Trump ta ce matakan za su shafi wasu bangarori masu muhimmanci ga tattalin arzikin Iran, ciki har da zinare, harkokin jiragen sama da kuma jigilar kayayyaki ta ruwa.
Asali: Legit.ng

