Abin Ya Yi Yawa: An Kai Mutane Wuya kan Tashin Farashin Buhun Siminti a Najeriya

Abin Ya Yi Yawa: An Kai Mutane Wuya kan Tashin Farashin Buhun Siminti a Najeriya

  • Masana sun ce ya kamata farashin siminti mai nauyin kilo 50 ya kasance tsakanin N7,000 da N8,000 a matakin masana’anta
  • Masu saye na biyan tsakanin N12,000 da N15,000 kan buhu guda, lamarin da ya jawo damuwa tsakanin yan Najeriya
  • Masana sun danganta tsadar da ƙarancin gasa tare da kira ga ƙarin masana’antun siminti a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - ’Yan Najeriya, musamman masu gina gidaje da ƙwararrun masana harkar gine-gine, sun ƙara matsa lamba kan kamfanonin kera siminti.

Sun nemi kanfanonin da su yi bayanin dalilin tashin farashin kayan, yayin da masana suka ce farashin buhun siminti mai nauyin kilo 50 bai kamata ya kasance tsakanin N7,000 zuwa N8,000.

Siminti.
Buhunan siminti na kamfanin Dangote a daya daga cikin rumbunan ajiyar yan kasuwa Hoto: Dangote Cement
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta ce wannan yanayi ya sake haifar da damuwa kan yadda ake tsara farashin siminti tun daga matakin kamfanoni zuwa wurraren da jama'a ke saye.

Kara karanta wannan

'A bar yan Najeriya su yanke hukunci': Bashir Ahmad ya kalubalanci Kwankwaso

Farashin siminti na ci gaba da tashi

Bayanai sun nuna cewa a halin yanzu masu saye ba biyan tsakanin N12,000 da N15,000 kan kowane buhu mai nauyin kilo 50, gwargwadon wurin da ake saye.

Farashin ya nuna gagarumin ƙaruwa daga kusan N7,500 da ake sayar da buhun siminti a ƙasa da shekara guda da ta gabata, duk da cewa Najeriya na da ƙarfin samar da siminti sama da tan miliyan 60 a shekara.

Masu ruwa da tsaki sun ce lamarin na ƙara tayar da hankali musamman ganin yadda ƙasar ke fama da ƙarancin gidaje da aka kiyasta ya zarce gidaje miliyan 15, yayin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin inganta samar da gidaje masu sauƙin kudi.

Yan Najeriya na neman karin bayani

Mai fafutukar samar da gidaje masu sauƙin kudi kuma masanin gine-gine, Ezekiel Nya-Etok, ya bayyana lamarin a matsayin “abin damuwa matuƙa”.

Ya ce ’yan Najeriya sun cancanci sanin dalilin da ya sa farashin muhimmin kayan gini watau siminti ya tashi sosai.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya kwantowa Tinubu kura kan batun maido tallafin man fetur

“Tambaya ce da ta cancanci amsa. Na yi imanin cewa ’yan Najeriya, musamman miliyoyin mutanen da ke fama wajen samun rufin asiri, sun cancanci wannan amsar,” in ji shi.

Nya-Etok, wanda kuma shi ne Daraktan Ayyukan Gidaje na Hukumar Gidaje ta Tarayya, ya amince cewa masu kera siminti na buƙatar dawo da kuɗaɗen da suka kashe wajen samarwa, saka jari a masana’antu, biyan ma’aikata da kuma samun riba.

Dalilin neman bayanin farashin siminti

Sai dai ya ce neman bayani ba ya nufin adawa da halastacciyar ribar da suke samu, illa dai neman gaskiya, gasa da kuma farashi mai sauƙi.

Ya yi kira da a bayyana yadda N15,000 da ake sayar da buhun siminti a kasuwa ta kasu, ciki har da kuɗin samarwa, albarkatun ƙasa, makamashi da man fetur.

Ya ce idan alkaluman suka nuna cewa N15,000 shi ne farashin da tattalin arziƙi ya tilasta, hakan zai taimaka wa ’yan Najeriya su fahimci dalilin, cewar rahoton Leadership.

Buhun siminti.
Buhunan siminti na kamfanin Dangote da ake kerawa a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: UGC

Sai dai idan binciken ya nuna cewa akwai wata riba da ba ta da assli, ya ce ya kamata a gano inda ake samun wannan riba da kuma wadanda ke amfana da ita.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yadda yan bindiga suka rika tashin mutane daga barci, su harbe su har lahira

Hakan dai ya biyo bayan wani bincike na farko da Hukumar FCCPC ta gudanar kan masana’antar siminti, inda hukumar ta ce ta gano alamun yiwuwar magudin farashin siminti.

Farashin buhun siminti ya tashi

A baya, kun ji cewa farashin buhun siminti ya tashi zuwa fiye da N10,500 a sassan Najeriya wanda hakan ya tsayar da ayyukan gine-gine da dama

Masu sayar da siminti a Legas suna zargin dillalai da tsawwala farashin simintin alhalin suna sayo shi da araha daga kamfan

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262