2027: Matan da Suka Fito Neman Kujerar Tinubu a Zaben Najeriya

2027: Matan da Suka Fito Neman Kujerar Tinubu a Zaben Najeriya

  • Mata biyu ne suka rage cikin masu neman kujerar shugaban Najeriya a zaɓen 2027, yayin da wasu ke neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa
  • ’Yan takarar sun fito ne daga fannoni daban-daban da suka haɗa da siyasa, kiwon lafiya, ayyukan jin ƙai, nishaɗi da kasuwanci
  • Daga cikin yan takarar akwai wacce aka tsayar da bayan an cimma yarjejeniyar da sauran yan takara domin karfafa wa mata gwiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Yayin da Najeriya ke shirin babban zaɓen 2027, wasu mata kaɗan amma masu tasiri sun fito domin neman damar taka muhimmiyar rawa a matakin siyasar ƙasa mafi girma.

Matan sun fito ne daga fannoni daban-daban, ciki har da ƙoƙarin haɗa kan jama’a a matakin ƙananan hukumomi, gudanar da jam’iyyu, kiwon lafiyar jama’a, ayyukan jin ƙai, harkar nishaɗi da kasuwanci.

Kara karanta wannan

APC: 'Dalilin Atiku na yin alkawarin dawo da tallafin man fetur idan an zaɓe shi'

Mata sun karu a neman kujerar shugabancin Najeriya fiye da baya
Esther Nkem Okereke ta NRM, Ada Elizabeth Fredrick Okwori ta NDP, Hajja Bintu Konto ta LP Hoto: Esther Nkem Okereke/Idoma Blueprint/Amb Sunday Chibuzo Okereke
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa sai dai bayyanar matan a wannan takara ta sake nuna yadda mata ke ƙara neman dama a matakin siyasa mafi girma a Najeriya.

Mata sun shiga neman takara

Trust Radio duk da cewa sauya Anita Zugwai-Chukwu da jam’iyyar YPP, wannan ya sa ta sa mata biyu kacal suka rage cikin masu neman kujerar shugaban ƙasa, bisa sabon ci gaban da aka samu.

Matan da ake ganin suna cikin neman kujera a zaɓen 2027 sun haɗa da Ada Elizabeth Fredrick Okwori ta NDP, Esther Nkem Okereke ta NRM, Hajja Bintu Konto ta LP da Ofordile Peace Egobia ta APP.

Mata sun takara a zaben 2026
Bintu Konto da abokin gaminta na takara a LP Hoto: Abia State Labor Party/Amb Sunday Chibuzo Okereke
Source: Facebook

Okwori da Okereke su ne masu neman kujerar shugaban ƙasa, yayin da Konto da Egobia ke takarar mataimakan shugaban ƙasa.

Haka kuma, Ndidi Patience Key an zaɓe ta a matsayin abokiyar takarar sabon ɗan takarar shugaban ƙasa da ya maye gurbin Zugwai-Chukwu a jam’iyyar YPP.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fito da bayani, an ji dalilin Atiku na ƙin sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

Yadda jam'iyyun suka tsayar da mata takara

Tun farko Zugwai-Chukwu ta kafa tarihi bayan YPP ta amince da ita ba tare da hamayya ba a matsayin mace ta farko da za ta wakilci jam’iyyar a takarar shugaban ƙasa.

An yi hakan ne a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ranar 30 ga Mayu, 2026. Sai dai daga baya jam’iyyar ta maye gurbinta da Peter Agada a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.

Ada Okwori, wadda ita ce shugabar jam’iyyar NDP ta ƙasa, ta samu tikitin takarar shugaban ƙasa ne bayan wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin sassan jam’iyyar daga sassa daban-daban na ƙasar.

Okwori ’yar kabilar Idoma ce daga Jihar Benue, ta daɗe tana harkar siyasa, inda ta taɓa kasancewa 'yar jam'iyyar PDP tare da gudanar da ayyukan haɗa kan jama’a a matakin ƙasa.

Ta kafa shirin Ward2Ward, wanda ke ƙarfafa mutane su shiga harkokin siyasa tun daga matakin al’umma. Saƙon siyasarta ya fi mayar da hankali kan ƙara shigar da jama’a cikin siyasa daga tushe.

Kara karanta wannan

ADC ta hango abin da zai jawo matsalar yan bindiga a Jigawa, ta gargadi gwamnati

Mace ta samu tikitin takara

A baya, mun kawo labarin jam'iyyar LP ta bayyana Bintu Konto a matsayin 'yar takarar mataimakin shugaban kasa don zaben shekara ta 2027 da ke tafe.

Macen ‘yar siyasar za ta kasance a tikiti tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Dr. Chibuzo Okereke. Hajiya Bintu Konto kwararriya ce a fannin lafiyar jama'a da ayyukan jin kai.

Dr. Chibuzo Sunday Okereke wanda malamin jami’a ne a Abuja ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP a watan Yuni na 2026 da ake ciki

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng