Ni ba barawo ne, na saci waya ne domin biyan kudin jarrabawar WAEC - Wani matashi

Ni ba barawo ne, na saci waya ne domin biyan kudin jarrabawar WAEC - Wani matashi

- Wani matashi dan shekara 20, James Egbe, ya gurafana gaban kotu saboda ya saci wayar salula

- Egbe ya amsa laifin satar da yayi, amma yace yayi satar ne domin ya samu damar biyan kudin jarabawa

- An yanke masa hukuncin wata 4 a gidan kaso ko ya biya tarar N10,000 tare da biyan mai yawar kudin wayar sa N24,000

Wani matashin dan shekara 20 mai suna James Egbe ya bayyana wa kotu da ke Abuja a ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu a kan cewa ya saci wayar salula domin ya samu damar biyan kudin jarabawar WASSCE.

Kamfanin dillanci labarai (NAN) ta bayyana cewa wanda ake zargin ya nuna nadamar sa sannan ya roki kotu da ta saukaka masa yayi alkawarin bazai kara aikata laifi ba.

Ni ba barawo ne, na saci waya ne domin biyan kudin jarrabawar WAEC - Wani matashi
Ni ba barawo ne, na saci waya ne domin biyan kudin jarrabawar WAEC - Wani matashi

KU KARANTA: Karshen alewa kasa: An yanke ma wani dan fashi da makami hukuncin kisa ta hanyar rataya

Alkalin kotun Muhammad Marafa ya yanke masa hukuncin watanni hudu a gidan kaso ko ya biya tarar N10,000.

Marafa ya bawa Egbe umarnin ya bawa wanda yai kara, Ani Obinna, N24,000, idan baiyi haka ba za'a kara masa watanni biyu a gidan kason. Yace babu wani sassauci ga duk wanda yayi laifi.

Mai shigar da karar, Babajide Olanipekun, ya bayyana wa kotu ce mai karar ya sanar dasu afkuwar lamarin ne a ranar 3 ga watan Afrilu.

Oladipekun yace Egbe ya tare wanda yayi karar ne a dai dai cocin St. Luke dake Kubwa, ya kuma kwace wayar sa kirar Tecno WX3 wadda takai N24,000 a ranar 31 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164