Gwamnatin Najeriya Ta Yi Magana bayan Ganin Kumfa a Kaduna
- Hukumar NESREA ta fara bincike kan wani sinadari da ake zargin ya zube a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan wani hatsarin mota
- NESREA ta tattara samfurin kumfar, ƙasa da ruwan rafin da ke kusa domin gwaji a dakin bincike saboda gano me ya faru a wajen
- Biyo bayan tattara bayanan, hukumar ta gargadi jama'a da su guji taɓa kumfar, ruwan da kuma ƙasar yankin har sai an kammala bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaduna – Hukumar Kula da Ka'idojin Muhalli ta Ƙasa (NESREA) ta fara bincike kan wani sinadari da ake zargin ya zube a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, lamarin da ya haifar da kumfa a wurin.
A cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar yaɗa labarai ta hukumar, Nwamaka Ejiofor, ta fitar, ta ce tawagar ofishin NESREA na Jihar Kaduna ta kai ziyara wurin domin gudanar da bincike.

Source: Facebook
A sakon da NESREA ta wallafa a Facebook, ta ce tawagar ta samu jagorancin shugaban hukumar a Kaduna, Hena Dangari Emmanuel.
Abin da binciken farko ya gano
A yayin ziyarar, jami'an NESREA sun gana da shugaban 'yan sanda na yankin Jere, ACP Sani Zubairu, da kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) na yankin, da kuma shugaban al'ummar yankin.
Binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ta yi hatsari, wanda ya jawo zubewar kayayyakin da take ɗauke da su a wurin.
Sai dai hukumar ta ce har yanzu ba a tabbatar da irin sinadarin da ya zube ba, saboda haka ake ci gaba da gudanar da bincike.
NESREA ta tattara samfur
Hukumar ta bayyana cewa ta tattara bayanai daga jami'an gwamnati da mazauna yankin domin taimakawa binciken da za a yi.
Haka kuma, ta ɗauki samfurin kumfar da aka gani, tare da samfurin ƙasa da ruwan wani rafi da ke kusa da wurin domin gudanar da gwaje-gwaje a dakin bincike.
An bayyana cewa sakamakon gwajin zai taimaka wajen gano ko sinadarin na da haɗari ga lafiyar jama'a da muhalli.
An yi gargaɗi ga jama'a
NESREA ta buƙaci jama'a da su guji kusantar ko taɓa farin kumfar, ruwan rafin da kuma ƙasar da ke kewaye da wurin har sai an kammala binciken.

Source: Facebook
Hukumar ta ce yin hakan zai taimaka wajen kare mutane daga yiwuwar kamuwa da illa idan har sinadarin ya kasance mai haɗari.
Ta kuma tabbatar da cewa za ta sanar da jama'a sakamakon binciken da zarar an kammala gwaje-gwajen da ake yi.
Dalung ya ce ta'aziyya Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiya Malama Ummulkhairi Usman Aliyu da aka kashe a Kaduna.
Dalung ya ce ya gana da mijinta, Malam Aliyu Muhammed, da 'ya'yansu, inda ya saurari irin halin ƙuncin da iyalin ke ciki bayan rasuwar marigayiyar.
Rahotanni sun ce an kashe Malama Ummulkhairi ne bayan wasu suka yi mata zargin ƙoƙarin sace yara, alhali tana neman kwatance ne zuwa wurin karatun addini.
Asali: Legit.ng

