Dubu Ta Cika: An Kama Wani Mutumi da Ake Zargi da Ƙulla Kasuwanci da Yan Bindiga a Katsina
- Dakarun rundunar 'yan sandan Katsina sun kama wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ga 'yan bindiga a jihar
- Jami'an tsaron sun kwato kwayoyin D5 guda 500 daga hannun wanda ake zargin, inda bincike ya nuna yana da alakar kasuwanci da yan bindiga
- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce za su ci gaba da lalata hanyoyin samar da kayan tallafin ga miyagun masu aikata laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama wani da ake zargi da kasancewa fitaccen dillalin miyagun kwayoyi da ke da alakar kasuwanci da 'yan bindiga.
Yan sandan sun gano cewa wanada ake zargin na kai wa yan bindigar da ke addabar karamar hukumar Funtua da yankunan da ke makwabtaka da ita, miyagun kwayoyi.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rajoto cewa rundunar yan sanda ta bayyana sunan wanda ake zargin da Sunday Eze, wanda aka fi sani da Dunbuje.
Yadda yan sanda suka kama Danbuje
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce jami'an da ke aiki a ofishin 'yan sanda na Funtua ne suka kama wanda ake zargin bayan samun sahihan bayanan sirri.
Ya ce an kama shi da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar 15 ga Yulin 2026 bayan jami'an sun bi sawunsa.
An kwato kwayoyin D5 guda 500
Aliyu ya bayyana cewa binciken da aka yi wa wanda ake zargin nan take ya kai ga gano kwayoyin D5 guda 500 da ake zargin an tanade su ne domin rabawa masu aikata laifuka.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya kware wajen samar wa 'yan bindiga da sauran kungiyoyin masu laifi miyagun kwayoyin da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Yan sanda na ci gaba da bincike
Rundunar ta ce wanda ake zargin na tsare a hannunta yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ke cikin wannan harka da kuma inda ake samo miyagun kwayoyin.
A rahoton Vanguard, Aliyu ya ce:
"Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike."
Kwamishina ya yabawa jami'ai
Kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami'an da suka gudanar da aikin cikin nasara.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da rusa hanyoyin da masu aikata laifuka ke samun kayan tallafi, musamman miyagun kwayoyi.

Source: Facebook
Hakazalika, ya bukaci mazauna jihar su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen yaki da laifuka a fadin jihar.
Sojoji sun cafke dan bindiga a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar kama wani da ake zargin ɗan bindiga a ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan
Rana ta baci: Ƴan bindiga sun yi arba da ƴan sanda bayan sun sace mutane a Sokoto
Rahotanni sun nuna cewa an kama wanda ake zargin mai suna Lawal Sani da a ranar 15 ga Yuli, 2026 lokacin da sojoji ke dawowa daga wani samame da suka kai a yankin Bakori.
An ce sojojin sun tsaya na ɗan lokaci a garin Yantumaki, inda suka ci karo da mutumin da suka ga alamun mai laifi ne, suka kuma fara gudanar da bincike a kansa.
Asali: Legit.ng

