'Yan Bindiga Sun Afkawa Bankuna Da Ofishin 'Yan Sanda, Sun Yi Barna Sun Tsere

'Yan Bindiga Sun Afkawa Bankuna Da Ofishin 'Yan Sanda, Sun Yi Barna Sun Tsere

- Wasu 'yan fashi sun afkawa bankuna a wasu yankunan jihar Osun, in da suka hallaka mutane

- Hakalila sun afkawa ofishin 'yan sanda a wasu yankunan kafin daga bisani aka fatattake su

- Shaidan gani da ido ya bayyana yadda lamarin ya faru, yana mai ba da bayanin harbe-harbe da ya ji

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari bankunan kasuwanci biyu da ofisoshin ‘yan sanda da yammacin Laraba a garin Apomu da Ikire da ke jihar Osun.

A yayin harin, an samu labarin cewa ‘yan fashin sun harbe mutane da yawa, duk da cewa rundunar 'yan sanda ta jihar ta ce ba ta samu adadin wadanda suka rasa rayukansu ba.

An ce barayin sun shiga Apomu da Ikire ta cikin garin Ikoyi kuma sun kasa kansu zuwa gungu daban-daban kafin su fara kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda da bankunan da abin ya shafa, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Baya Ga Korona, Wata Sabuwar Cuta Ta Sake Bullowa a Kasar China Daga Kajin Gona

'Yan Bindiga Sun Afkawa Bankuna Da Ofishin 'Yan Sanda, Sun Yi Barna Sun Tsere
'Yan Bindiga Sun Afkawa Bankuna Da Ofishin 'Yan Sanda, Sun Yi Barna Sun Tsere Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wani ganau da ke zaune a Apomu, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce ya ji karar harbe-harbe misalin karfe 5:30 na yamma a kusa da harabar wani banki da ke Unguwar Oke-Ola.

A cewar wani mazaunin Ikire, wanda aka bayyana sunansa da Oloruntoyin, ‘yan fashin sun kai hari wani banki da ke kusa da fadar Akire, da kuma ofishin 'yan sanda na Ayedaade.

Ya ce daga baya barayin kuma suka bar garin suka gudu bayan da wasu mafarautan yankin da ‘yan sanda suka yi artabu da su.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da harin da aka kai a wani banki a Apomu, ofishin 'yan sanda da ke Ikire, da kuma yankin Ikire na ’yan sanda da 'yan fashi suka afkawa.

Ta ce amma ba a samu adadin wadanda suka mutu ba, sai dai rahoton jaridar Guardian ya bayyana cewa, mutane biyar ne suka rasa rayukansu a yayin harin.

KU KARANTA: Ba Sauran Cece-Kuce: Majalisa Ta Amince Da Daidaita Kwalin HND Da Na Digiri

A wani labarin, Kungiyar masu noma Albasa da Kasuwancinta a Najeriya (OPMAN) ta bayyana kudurin ta na dakatar da samar da albasa ga yankin Kudu maso Gabas saboda yawaitar rashin tsaro.

Shugaban kungiyar OPMAN na kasa, Aliyu Isah, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 2 ga watan Yuni, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce kungiyar ta yanke shawarar ne biyo bayan sace motocin mambobinsu biyu da ‘yan bindiga suka yi wadanda suke zargin mambobin kungiyar masu fafutukar kafa haramtacciyar kasar Biafra ce ta IPOB suka aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel