Daga karshe kungiyar IPOB ta bayyana masu daukar nauyinta

Daga karshe kungiyar IPOB ta bayyana masu daukar nauyinta

  • Kungiyar awaren IPOB ta bayyana wadanda suke mara mata baya tare da daukar dawainiyarta ta bangaren kudi
  • IPOB ta bayyana cewa babu wani mutum daya da zai iya daukar dawainiyarta illa tana samun tallafinta daga miliyoyin 'yan uwa na gida da waje
  • Ta kuma yi hannunka mai sanda a kan zarginta da ake yi da kai hare-hare a jihar Imo da yankin kudu maso gabas

Imo - Bayan shafe tsawon shekaru da dama ana bincike, kungiyar 'yan aware ta Biyafara wacce aka fi sani da IPOB ta bayyana wadanda suke mara mata baya tare da daukar dawainiyarta ta bangaren kudi.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Emma Powerful, IPOB, ta tabbatar da cewa babu wani mutum daya da zai iya daukar nauyin kungiyar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

Daga karshe kungiyar IPOB ta bayyana masu daukar nauyinta
Daga karshe kungiyar IPOB ta bayyana masu daukar nauyinta

Kungiyar wacce Mazi Nnamdi Kanu ke jagoranta ta bayyana a jawabinta cewa:

"Sace Uche Nwosu ya fallasa wadanda ke haddasa rashin tsaro a jihar Imo, cewa abun da ya faru da Nwosu a ranar Lahadi ya tabbatar da kungiyar. Wannan wani tabbaci ne cewa IPOB da ESN ba sune ke da alhakin hare-hare da sace mutane a jihar Imo ba sabanin zargin karya da farfaganda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Amma Allah madaukakin sarki, Chukwu Okike Abiama, ya fallasa su a wannan karon."

Kan wanda ke daukar nauyin kungiyar, ta ce:

"A karo na goma-sha, babu wani mutum daya da zai iya daukar nauyin kungiyar IPOB. Mu kungiya ce ta duniya kuma miliyoyin 'yan uwanmu na gida da waje sune ke daukar dawainiyarmu.
"Ba mu taba boye wannan gaskiyar ba saboda mu ba boyayyiyar kungiya ko ta 'yan ta'adda bane. IPOB na da karfi sosai kuma ba ma bukatar Okorocha, Uche Nwosu ko Hope Uzodinma ko kuma wani dan siyasa ya dauki nauyin mu. Ba ma da hadi da barayin yan siyasa ko mutane da suka tara dukiyarsu ta haram."

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Sai dai kuma a kan kama dan takarar gwamnan jihar Imo a 2019 na jam’iyyar Action Alliance, AA, Uche Nwosu a cocin St Peter’s Anglican a ranar Lahadi, kungiyar ta yi Allah wadai da lamarin.

Ta ce:

"Yanzu a bayyane yake game da wadanda suke sace-sace/kashe-kashen sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da 'yan siyasa a jihar Imo da sauran yankunan kudu maso gabas."

'Yan sanda sun kama surukin Okorocha a cikin coci a Imo

A wani labarin, mun kawo a baya cewa an shiga rudani a cocin St Peters da ke Eziama Obire a karamar hukumar Nkwere na jihar Omo, a ranar Lahadi, a lokacin da aka kama Uche Nwosu, surukin Sanata Rochas Okorocha.

Yayin yadda aka kama shi ya janyo mutane suke tunanin kama sace Nwosu aka yi. A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga mutane da bindiga suna awon gaba da Nwosu, a lokacin da ya hallarci addu'ar da ake yi bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Kwamandan ISWAP, Abou Maryam, ya sheka barzahu sakamakon luguden sojin NAF

An ji muryar wasu mutane a bidiyon suna cewa 'An sace Nwosu'. An sace Ugwumba.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel