Nnamdi Kanu: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Shugaban Kungiyar IPOB

Nnamdi Kanu: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Shugaban Kungiyar IPOB

  • Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi bayar da belin Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB
  • Kotun ta bayar da umarnin a gaggauta ci gaba da shari’ar da ake yi kan shugaban ƙungiyar ta IPOB, wanda ake zargi da laifin cin amanar ƙasa
  • Kanu, wanda hukumar DSS ta tsare tun bayan kama shi a watan Yunin 2021, ya gurfana a gaban kotun a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar neman belin Nnamdi Kanu, jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra.

A maimakon hakan sai mai shari’a Binta Nyako ta yanke shawarar gaggauta ci gaba da sauraron shari’ar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya bayyana ɗan takarar da zai lashe zaben gwamnan jihar Edo a 2024

Kotu ta ki bada belin Nnamdi Kanu
Kotu ta ki amincewa da bukatar bada belin Nnamdi Kanu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A baya lauyan Kanu, Alloy Ejimakor, ya buƙaci a bayar da belinsa kafin a fara shari’ar a ranar Talata 19 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake so a bada belin Nnamdi Kanu?

Ejimakor ya nuna damuwarsa kan yadda lafiyar Kanu ke ƙara tabarbarewar, inda ya yi gargaɗin cewa ci gaba da tsare shi da hukumar DSS ke yi na da matuƙar hatsari ga rayuwarsa, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Bugu da ƙari, Ejimakor ya ƙara da cewa ci gaba da tsare Kanu a gidan yari zai kawo masa cikas wajen kare kansa a gaban kotun da hujjoji masu ƙarfi.

Lauyan gwamnati ya yi watsi da buƙatar

Sai dai, lauyan da ke wakiltar gwamnatin tarayya, Adegboyega Awomolo (SAN), ya bayar da shawarar yin watsi da buƙatar belin, sannan ya buƙaci a gaggauta yi masa shari’a.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

Awomolo ya bayyana cewa akwai cibiyoyin kiwon lafiya a hukumar DSS waɗanda za su iya kula da lafiyar Kanu.

Awomolo ya yi zargin cewa Kanu, wanda a baya ya tsallake beli, bai bayyana gaskiya a cikin takardun da lauyoyinsa suka gabatar cewa ba zai gudu ba idan har aka bayar da belinsa.

A baya dai an bayar da belin Kanu saboda dalilai na rashin lafiya a ranar 25 ga watan Afrilu, 2017, bayan ya shafe watanni 18 a tsare.

Sai dai, bayan bayar da belin nasa ya tsere inda ya fice daga ƙasar nan.

Kotu ta yi hukunci kan makomar Kanu

A baya rahoto ya zo cewa Kotun Ƙoli ta warware hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi na wanke shugaban shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Bayan yin watsi da hukuncin, kotun ta kana ta amince a ci gaba da tuhumar Kanu kan ƙarar zarginsa da hannu a ayyukan ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel