2027: Minista Ya Fadi Abin da Ya Kamata Musulmai Su Yi Wa Tinubu
- Ministan ayyukan tarayya, Sanata David Umahi, ya yi buɗa baki tare da al'ummar Musulmai a gidansa da ke jihar Ebonyi
- David Umahi ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga al'ummar Musulmai su marawa shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan na jihar Ebonyi ya bayyana shugaba Bola Tinubu yana da kyakkyawar manufa kan ci gaban Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya miƙa ƙoƙon bararsa ga al’ummar Musulmi kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
David Umahi ya buƙaci al'ummar Musulmi da su ci gaba da yi wa Tinubu addu’a da kuma ba shi cikakken goyon baya domin samun nasarar sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Facebook
Ministan ya yi wannan bayanin ne a gidansa da ke Abakaliki a daren ranar Lahadi, yayin da yake yin buɗa-baki tare da Musulmai mazauna jihar Ebonyi, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya buƙaci Musulmai su zaɓi Tinubu
Umahi ya bayyana cewa abubuwa sun fara canzawa a ƙasar nan ƙarƙashin mulkin Tinubu, kuma manufofin da yake da su za su sanya ƴan Najeriya farin ciki.
Ya jaddada cewa an wuce lokacin shan wuya a ƙasar nan, domin Allah yana nuna ƙarfinsa da ikonsa ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu.
“A cikin addu’o’inku, ku yi wa shugaban ƙasa addu’a domin nasararsa da kuma duk ayyukan alheri da yake aiwatarwa."
“Mu na roƙon Allah ya ba shi lafiya da nasara, kuma duk alheran da yake fatan cimmawa ga wannan ƙasa, Allah ya ba shi ikon aiwatar da su."
"A lokacin da muke shirin kammala wa’adin farko, muna addu'ar Allah ya ba shi damar zarcewa don kammala kyawawan ayyukan da ya fara."
"Abubuwa na canzawa, Allah yana nuna ikonsa a cikin wannan gwamnati, kuma mafi munin lokaci ya wuce. Allah yana taimakonmu."
- David Umahi
Umahi ya buƙaci a yi wa gwamnan Ebonyi addu'a
David Umahi, wanda tsohon gwamnan jihar Ebonyi ne, ya kuma buƙaci al’ummar Musulmi su yi addu’a ga gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru.
"Gwamnan jihar Ebonyi ya samar da zaman lafiya, babu sauran hamayya a jihar Ebonyi. Jam’iyyar APC ce kawai take a jihar Ebonyi, ya haɗa kowa a cikin inuwa ɗaya."
“Gwamnan yana yin bakin ƙoƙarinsa wajen ci gaban jihar. Ku yi masa addu’a domin Allah ya kare shi, ya ba shi nasarar kammala wa’adinsa na shekaru huɗu, kuma ya ba shi nasara don samun wa’adi na biyu."
“Allah ya ɗaukaka jihar Ebonyi, ya sanya mu zama na ɗaya a ƙasa baki ɗaya, a fannin zaman lafiya, wadatar arziki, da ingantaccen mulki."
- David Umahi
Tsohon ɗan majalisa ya koma saboda Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani tsohon ɗan majalisar wakilai a jihar Edo, Nicholas Ossai, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan
"Ɗan takara 1 tal gare mu," Sanatan APC ya hango wanda zai ci gaba da mulkin Najeriya a 2027
Nicholas Ossai ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar APC ne domin nuna goyon baya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng