Manyan 'yan Arewa 5 da ba za'a manta da su ba a tarihi

Manyan 'yan Arewa 5 da ba za'a manta da su ba a tarihi

Akwai masu girma yan yankin Arewacin kasar guda biyar wadanda yan Najeriya kuma suna tunaninsu kullum saboda abubuwa masu kyau sunyi a yayinda suka duniya.

(1) Ahmadu Bello Sardauna

Manyan 'yan Arewa da ba za'a manta da su ba a tarihi

An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan Yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya.

Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na daya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.

Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966. Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.

An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo suka jagoranta.

(2) Malam Aminu Kano

 “Nijeriya daya ce, amma kowa ya san gidan tsohonsa.” Wannan ne lafazin da ya fi yin kururuwa a kunnuwan ’yan Nijeriya musamman a Arewa, wadanda Malam Aminu Kano ya furta su a lokacin gwagwarmayar siyasa zamanin ya na raye. Karara kalaman sun nuna cewa, ya yi gwagwarmaya domin kare muradun yankin Arewa, wanda ya fito daga cikinsa.

An haife shi ne a shekarar 1920 a gidan Malam Yusuf, wanda mahafin nasa malamin addini ne daga zuri’ar Fulanin Gyanawa a birnin Kano kuma muhutin alkali. Aminu Kano ya halarci Kwalejin Katsina (Katsina College), inda kuma daga bisani ya tafi Jami’ar London (University of London) sashen koyon ilimi malanta na Institute of Education tare da Sir Abubakar Tafawa balewa. Firaministan Nijeriya na farko. Bayan ya kammala Kwalejin Katsina ya sami takardar shaidar malanta sai ya fara aiki a matsayin malamin makaranta a Bauchi Training College.

Duk da cewa, ya fi shekara talatin da rasuwa, amma har yanzu ’yan siyasa su na amfani da hotunansa wajen tallen takararsu a garuruwa daban-daban na Arewa, musamman birnin Kano, wanda ya fi kowane birni girma da yawan jama’a a yankin arewacin Nijeriya.

Tabbas Malam Aminu Kano ya shuka abin alheri; don haka ne ba za a taba mancewa da alherinsa ba. Har ya rasu bai tara dukiya ba duk da cewa ya rike mukamai da dama a kasar. Allah Ya ka rahama maknwancinsa. Amin.

(3) Sir Abubakar Tafawa-Balewa

Manyan 'yan Arewa da ba za'a manta da su ba a tarihi

An haifi Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Najeriya a shekarar 1912.

Ya kasance mutum mai da'a da kuma asali kasancewar mahaifinsa ma'aikaci ne ga hakimin garin. Yayi karatu a makarantar horon malamai ta Katsina daga ( 1928 zuwa 1933), sannan ya zamo malami, kuma shugaban makarantar Bauchi Middle School.

Yayi karatu a makarantar horas da malamai ta London daga ( 1945 zuwa 1946), inda ya samu shaidar malanta.

A lokacin yakin duniya na biyu ya nuna sha'awarsa ta shiga harkokin siyasa, inda ya kafa zauren tattaunawa na Bauchi Discussion Circle.

Sannan daga bisani ya shiga siyasar malamai inda aka zabe shi mataimakin shugaban kungiyar malaman Arewa.

A shekarar 1952 ya zamo ministan ayyuka na Najeriya, ministan sufuri a 1954, sannan ya zamo jagoran jam'iyyar NPC a majalisar wakilai ta kasa.

Ya zamo Fira Ministan farko na Najeriya bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960.

A shekarar 1966, wasu sojoji suka yi kokarin juyin mulki inda anan ne aka sace shi kafin daga bisani aka kashe marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa.

(4) Murtala Muhammad

Manyan 'yan Arewa da ba za'a manta da su ba a tarihi

Gen. Murtala kusan ya shafe kwanaki 199 a kan kujerar shugabancin kasar nan a matsayinHead of state, ya hau mulki daga 29 ga watan yuli 1975, zuwa 13 ga watan fabrairu 1976.

Murtala shi ne mutum na biyar a jerin shugabannin kasar nan goma sha biyar, a iya tsawon kwanakin da ya shafe yana shugabanci bai kama ko kadangare ya daureba da sunan tuhumarsa da cin amanar kasa kusa tarihi ya nuna cewa shi ne shugaban da bai taba daure kowaba a mulkin wannan kasar, haka kuma shi ne mutumin da ya fara assasa cewa mulki zai koma hannun farar hula, wanda mataimakinsa da ya dora daga inda ya tsaya Gen. Olushegun Obasanjo ya cika wannan alkawari a shekarar 1977 inda Shehu Aliyu Shagari ya zama zababben shugaban kasa, haka kuma shi ne ya kirkiro jihohi da dama da kuma inganta al’amarin kananan hukumomi, haka nan kuma shi ne mutumin da ya kafa harsashin maida cibiyar mulki daga Legas zuwa tsakiyar Najeriya inda ake kira Abuja, yanzu mutumin da ya yi wadan nan muhimman ayyukan ya dace tarihi ya mance da shi?

Ko shakka babu amsar zata zama a’a, don haka ya zama dole gwamnati ta yi wani tsari domin koyar da yara halayyar mutanan kirki irinsa.

(5) Umaru Musa Yar'adua

Manyan 'yan Arewa da ba za'a manta da su ba a tarihi
Yar'adua resolved the Niger Delta crisis through dialogue

Shi dai marigayi Malam Umaru Babangida Musa 'Yar'Adua, an haifeshi ne a ranar 16 ga watan Augustan 1951 a birnin Katsina dake arewacin Najeriya. Mahaifinsa shine tsohon ministan birnin Lagos na farko a jamhuriya ta farko, kuma kafin ya rasu shine Matawallen Katsina, sarautar da kuma shi ma marigayi Umaru Musa 'Yar'Adua ya gada.

Marigayin ya fara makarantar Firamare ta Rafukka a 1958 kafin a mayar da shi makarantar Firamare ta kwana dake Dutsen Ma a 1962. Ya kuma halarci kwalejin gwamnati dake Keffi daga 1965 zuwa 1969. Sai kwalejin Barewa 1971, inda ya samu takardar shedar karatu ta HSC.

A lokacin da marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'Adua ya shiga siyasa ya yi hannun riga da mahaifinsa wanda a wancan lokaci yake mataimakin shugaban Jam'iyar NPN, inda shi kuma ya zama wakili a jam'iyar PRP ta Malam Aminu Kano mai adawa da NPN. A lokacin da Janar Babangida ya kaɗa gangar siyasa ya zama sakataren jam'iyar SDP a jihar ta Katsina kuma ɗan takararta na gwamna, amma kuma ɗan takarar jami'iyar NRC na wancan lokaci Malam Saidu Barda ya kada shi. To sai dai a 1999 Malam Umaru Musa 'Yar'Adua ya tsaya takakarar muƙamin gwamnan jihar ta Katsina kuma ya samu nasara a ƙarƙashin jam'iyar PDP, haka kuma ya sake nasara a zaɓen 2003.

A shekarar 2007 Umaru Musa 'Yar'Adua ya zama ɗan takakar muƙamin shugaban ƙasa na Jam'iyar PDP bayan ya samu taimakon tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya zama shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2007.

Marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'Adua ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2010 da muke ciki a fadar gwamnati dake Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida daga Saudiya inda yake jinya.

Ya kuma rasu ya bar mahaifiyarsa da 'yan'uwa da matar aure guda Hajiya Turai tare da 'ya'ya bakwai da ya haifa da ita da suka haɗa da mata biyar da maza biyu. Haka kuma yana da wasu 'ya'ya biyu maza da matarsa ta biyu Hajiya Hauwa Umar Radda.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel