Ganduje Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Musabbabin Abin da Ya Jefa Arewa a Matsala

Ganduje Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Musabbabin Abin da Ya Jefa Arewa a Matsala

  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya fayyace babban matsalar da Arewacin Najeriya ke fuskanta
  • Shugaban APC ya ce yawan rashin ilimi a tsakanin al'ummar Fulani shi ne babban matsalar da yankin ke fuskanta da sauyin yanayi
  • Legit Hausa ta tattauna da wani Fulani wanda ya yi tsokaci kan wannan lamari da Ganduje ya yi martani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya fadi babban dalilin matsalar da ke damun Arewa.

Ganduje ya ce sauyin yanayi da ya tilasta Fulani zuwa wasu ɓangarorin kasar ya na daga cikin matsalolin yankin Arewacin Najeriya.

Ganduje ya bayyana musabbabin matsalar Arewacin Najeriya game da Fulani
Dakta Umar Ganduje ya ce rashin ilimi a tsakanin Fulani shi ne babban matsalar Arewa. Hoto: @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

Fulani: Ganduje ya fadi matsalolin Arewa

Kara karanta wannan

Fubara vs Wike: An yi kira ga Bola Tinubu ya tsoma baki kan rikicin siyasar jihar Rivers

Shugaban jam'iyyar ya kara da cewa yawan rashin ilimi a tsakanin al'ummar Fulani a yankin na daga cikin manyan kalubalen yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne a Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto yayin taron gasar wakokin Fulfulde, cewar rahoton Leadership.

Ya ce a da can baya akwai alaka mai kyau tsakanin Fulani da manoma kafin komai ya dagule a yanzu.

Martanin gwamnan Sokoto kan matsalar tsaro

A martaninsa, Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya ce gwamnatinsa ta na kokarin samar da kariya ga al'umma wurin dakile matsalolin tsaro.

Aliyu ya ce za su ci gaba da ba da kulawa sosai wurin tabbatar da samun zaman lafiya tare da dinke dukkan ɓarakar da ke tasowa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake yawan samun matsala tsakanin Fulani da manoma musamman a Arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

"Yana da kyau amma...": Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan harajin CBN

Legit Hausa ta tattauna da wani Fulani wanda yanzu babban ma'aikacin banki ne kan wannan lamari.

Mohammed Lawal ya ce wadannan kalamai na Ganduje tabbas gaskiya ne kan wasu matsaloli da Fulani ke fuskanta.

"Sauyin yanayi tabbas ya kawo tsaiko a rayuwar Fulani wanda ya jawo rigima kan wuraren kiwo da sauransu."
"Rashin ilimi ma ya kara matsalar saboda rashin samun damarmaki domin inganta rayuwarsu."

- Mohammed Lawal

Lawal ya ce sauran matsalolin sun hada da nuna musu wariya a siyasance da matsalar tattali arziki fadace-fadace kan iyaka da kuma matsalar tsaro.

An maka Abdullahi Ganduje a kotu

A wani labarin, wani tsohon mai neman takarar kujerar Dakta Abdullahi Ganduje ya maka shi a kotu kan shugabancin jam'iyyar.

Mohammed Sa'idu-Etsu ya ce tsarin da aka bi wurin nada shugaban APC ya sabawa doka inda ya bukaci a dauki mataki kan tsohon gwamnan.

Wannan na zuwa ne yayin da Ganduje ke cikin mawuyacin hali bayan neman dakatar da shi da aka yi ta yi a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel