Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

  • Abba Kabir Yusuf ya yi Allah-wadai da wadanda suke satar kaya a wuraren daga gwamnatinsa ta rusa
  • Sabon Gwamnan ya ce a hukunta wanda samu da laifin satar kayayyakin jikin wani gini da aka ruguza
  • Mai girma Gwamnan ya fitar da jawabi, ya na cewa ko wanene aka cafke, zai gamu da fushin hukuma

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi, ta na jan-kunnen masu satar dukiyar jama’a yayin da aka ruguza wasu gine-gine.

Abba Kabir Yusuf ya yi magana ta bakin babban sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, yana mai tir da danyen aikin wasu mutanen jihar.

Ganin abin da yake faruwa, Mai girma Gwamnan ya yi umarni ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da ya yi gaggawar kama masu wannan aika-aikar.

Abba Gida Gida
Sabon Gwamnan Kano, Abba Gida Gida da Mataimakinsa Hoto: sanusi.dawakintofa
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a gamu da fushin hukuma

Bugu da kari, Gwamnan ya bukaci doka tayi maza tayi aiki a kan duk wadanda aka samu da laifi.

Kamar yadda sanarwar Sanusi Bature Dawakin Tofa ta nuna, Abba Gida Gida kamar yadda aka fi saninsa, ya yi kira ga al’umma su zama masu bin doka.

A cikin takaici, Gwamnatin jihar Kano ta lura dabi’ar wasu da ke kokarin lalata dukiyar al’umma da sunan daukar ganima a ragowar gine-ginen da gwamnatin jiha ta ruguza a rushe-rushen da aka yi na gine-ginen da suka saba doka wanda tsohuwar gwamnati ta amince aka yi.
Saboda haka, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi umarni ga Kwamishinan ‘yan sanda na jiha da ya yi gaggawar kama duk wanda aka samu da wannan aika-aika, kuma a tabbata doka tayi aiki a kan su.

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Gidan rediyon Freedom ya ce wannan sanarwa ta gargaɗi ta fito ne daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Kano watau Dr. Abdullahi Baffa Bichi.

Jawabin ya kara da cewa Gwamnati mai-ci ta zo yin aiki ne domin ci gaban Kano ba bada lasisin rushe gine-gine da sace kayan mutane haka kurum ba.

A shirya bincike

An ji labari kungiyar ‘Yan takaran ‘yan jam’iyyar PRP a Kano zaben 2023, ta na rokon a binciki abubuwan da suka faru a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje.

Wadannan ‘yan siyasa sun taya Mai girma Abba Kabir Yusuf murnar rantsar da shi, sun ba shi shawarar ya cigaba da duk wasu ayyukan alheri a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel