Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi

Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi

- Iklima Musa matar aure ce daga jihar Filato wacce kishiyarta ta watsawa tafasasshen ruwan zafi

- Kishiyar Ilkima mai suna Justina ta watsa mata ruwan zafi a jiki bayan fadan da suka yi aka raba su

- Kamar yadda Iklima tace, ta tabbatar da cewa ba za ta taba yafewa da wannan barnar da aka yi mata

Iklima Musa tana neman a karbar mata hakkinta daga wurin kishiyarta wacce ta watsa mata tafasasshen ruwa a jihar Filato, Linda Ikeji ta wallafa.

Idan za mu tuna, wacce ake zargi da aika-aikar mai suna Justina Peter ana nemanta ido rufe bayan lamarin da ya faru a Gindiri a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

An gano cewa matar bata taba shiri da Iklima ba tun bayan da mijinta ya aurota a matsayin mata ta biyu a shekaru uku da suka gabata.

KU KARANTA: Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari

Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi
Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana, bayan kishiyoyin sun fara fada, mijinsu mai suna Ate Peter Manomi ya raba su.

Yayin da Iklima ta fito daga dakinta domin kwashe shanyarta, Justina ta watsa mata tafasasshen ruwan zafi.

Wannan harin ya bar Iklima da miyagun kuna a jikinta. Mijinsu Manomi, ya gaggauta mika Iklima asibiti kuma aka kwantar da ita.

"Na duka kasa in kwashe kayana da na wanke, ban san cewa ksihiyata ta taho ba da muguwar niyya. Ban taba tsammanin haka ba saboda an raba mu fadan.

"A lokacin da nake tashi tsaye, ta watsa min ruwa inda na fara ihu. Mijinmu ne ya fara zuwa. Inda nayi sa'a bai yi nisa ba. Da baya kusa da bamu san me zai faru ba." ta bayyana.

KU KARANTA: Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan

A wani labari na daban, 'yan sandan Najeriya sun sake damke mawallafin Sahara reporters, Omoyele Sowore a kan jagorantar wata zanga-zanga da yayi a babban birnin tarayya na Abuja.

Sowore tare da wasu 'yan gwagwarmaya sun shiga hannun 'yan sandan bayan da suka fito zanga-zanga mai suna #CrossoverWithProtest, zanga-zangar da suka shirya a dukkan fadin kasar nan ana gobe sabuwar shekara.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka arce ne suka tabbatarwa da Premium Times cewa an damke Sowore inda aka jefa shi daya daga cikin motocin 'yan sanda bakwai da aka tura wurin zanga-zangar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel