Iran Ta Yi Kwanton Bauna Ta Farmaki Amurka da Dare, Ta Wargaza Jirage
- Jiragen yaƙin Amurka da dama sun samu lahani bayan wani harin makamai da Iran ta kai kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan
- Rahoto ya ce jirgin A-10 Thunderbolt ɗaya ya rasa fikafikansa, yayin da kusan jiragen F-15 takwas suka samu ƙananan lahani
- Iran ta ce za a iya kawo ƙarshen yaƙin idan Amurka ta cika wasu sharuda, ciki har da janye sojojin Isra’ila daga Lebanon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Jiragen saman sojin Amurka da dama sun samu lahani sakamakon wani harin da Iran ta kai da daddare kan wani sansanin sojin Amurka da ke Jordan.
Wani jirgin A-10 Thunderbolt, wanda aka fi sani da Warthog, an kai masa hari har aka rasa ɗaya daga cikin fikafikansa, yayin da kusan jiragen F-15 guda takwas suka samu ƙananan lahani.

Source: Getty Images
Rahoton Reuters ya ce an kai harin ne a sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti, inda wasu daga cikin jiragen da suka samu lahani.
Rahoton ya ce sojojin Amurka da ke Jordan sun harba makamai masu linzami na Patriot sama da 30 domin kare kansu daga hare-haren Iran.
Ya ƙara da cewa harin ya faru ne bayan Amurka ta kai hari kan jiragen dakon mai guda biyar na Iran, lamarin da ya biyo bayan zargin Iran da kai hari kan wani jirgin ruwan yaƙin sojin ruwan Amurka.
A martanin da ta mayar, Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ce ta kai hare-hare kan jiragen dakon mai guda takwas da kuma jiragen ruwan yaƙi guda biyu, ciki har da sansanin Amurka da ke Jordan.
Bayanin da Iran ta yi
Amurka na da jiragen yaƙi da dama da ke aiki daga sansanin Muwaffaq Salti, wanda ke zama muhimmin sansanin da ake amfani da shi wajen gudanar da ayyukan soji kan Iran.
A wata sanarwa, Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ce ta kai “mummunan harin makamai masu linzami” kan sansanin Al-Azraq na Amurka da ke Jordan.
Rahoton ND TV ya nuna cewa Iran ta ce harin wani ɓangare ne na abin da ta kira “aikin ramakon gayya”.
Ta kuma ce ta kai hari kan jiragen ruwa sama da 12 da ke ƙoƙarin wucewa ta Mashigar Hormuz, yayin da ta sanar da faɗaɗa yankin da ta hana zirga-zirga a wajen mashigar da ta ce ta daɗe tana killacewa.
Bayanin da kasar Jordan ta yi
Jim kaɗan bayan harin, sojojin Jordan sun ce tsarin kariyar sararin samansu ya gano makamai masu linzami masu cin dogon zango guda 20 da ke shigowa.
A cewar sanarwar sojojin Jordan, an samu nasarar lalata 18 daga cikinsu, yayin da biyu suka faɗa a wuraren da babu mazauna.
Batun kawo karshen yakin
Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta bayyana cewa za a iya kawo ƙarshen yaƙin idan Washington ta cika wasu sharuda da ta gindaya.

Source: Facebook
Daga cikin sharuddan akwai dakatar da sabbin barazanar kai hari, janye sojojin Isra’ila daga Lebanon, sakin Dala biliyan 24 na kadarorin Iran da aka daskarar da su, da kuma daina tsoma baki kan shirye-shiryen nukiliya da makamai masu linzami na Iran.
An kai hari kasar Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa Houthi da Iran ke mara wa baya a Yemen sun kai wani gagarumin hari kan kudu maso yammacin Saudiyya.
Rahotanni sun bayyana cewa Harin ya ƙara tsananta rikicin yankin, inda jami’an Saudiyya suka ce an jikkata fararen hula da dama.
Sabon harin ya ƙara tsananta rikicin Saudiyya da Houthi, wanda ya sake barkewa a watan Yuli bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.
Asali: Legit.ng


