'Rungumar Mata': Soja Boy Ya Fito da Wata Gaskiya da Aka Kore Shi daga Kannywood
- Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da Usman Soja Boy saboda korafe-korafen batsa a bidiyonsa, musamman rungumar mata
- Soja Boy ya bayyana cewa Kannywood ba ta taɓa taimakA masa ba, sai dai shi ne ke taimakon masana’antar ta hanyoyi daban-daban
- Mawakin ya ce dakatarwar ba ta da tasiri a kansa, domin shi ya riga ya samu daukaka da kudi ba tare da taimakon Kannywood ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Da alama dai korar da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta yiwa jarumi kuma mawaki Usman Soja Boy ba za ta yi wani tasiri ba.
Soja Boy ya ce korarsa daga Kannywood kamar 'wasan yara' ne, tun da dama can shi ne ke taimakon 'yan masana'antar ba akasin haka ba.

Asali: Instagram
A cikin wani bidiyo da shafin Jakadiyan Arewa ya wallafa a shafinsa na Instagram, an ji Soja Boy na cewa Kannywood ba ta tsinana masa komai ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya faru Soja Boy ya ke maganganu?
Idan ba ku manta ba, Legi Hausa ta rahoto cewa hukumar tace fina-finai ta Kano ta ce ta karɓi korafe-korafe da dama kan mawaki Usman Soja Boy saboda batsa da yake yi a bidiyonsa.
Rungumar mata a bidiyo kusan shi ne babban dalilin hukumar na dakatar da mawakin tare da wasu jarumai mata da ke fitowa a bidiyonsa na baya-bayan nan.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya sanar da manema labarai a Kano cewa dakatarwar ta fara aiki nan take.
Dakatarwar na da tasiri ga Soja Boy?
Sai dai jarumi kuma mawaki, Usman Soja Boy ya ce wannan dakatarwar ko a kwalar rigarsa, domin Kannywood ba ta taba taimakonsa ba, shi ne ma ya taimake ta.
"Ace an kore ni daga harkar Kannywood, abun ban dariya ne. Babu mutum kwara daya da ya taba kirana ya saka ni fim ya biyani kudi, ko biya mun kudin otel.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
"Idan kora ne, sai dai ni na kori Kannywood, domin ni babu wani wuri kwara daya da Kannywood ta taba taimako na."
Soja Boy ya ce 'yan Arewa ne ba su san shi ba sai da ya fara fitowa a fina finan Kannywood irinsu Na Ladidi, Yahoo Boy, amma shi ya dade da yin suna a duniya.
"Da kudina aka gan ni" - Usman Soja Boy
Usman Soja Boy ya kara nanata cewa babu wani abu da Kannywood za ta iya yi masa, walau ta fuskar daukaka ko samun kudi, domin shi ya dade da wuce wajen.
"Duk wanda ya ganni a Kannywood, to da shirya fim ya ganni. Duk wanda ya ganni a Kannywood ya ga ina ciro kudi ne in sanya in yi fim.
"Babu mutum daya da zai ce ya zo ya yiwa Usman aiki kyauta, ko kuma na kira Usman na sanya shi a fim an sanshi a duniya, babu shi."

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
- Soja Boy
Mawakin ya ce duk wanda aka ga ya shiga fim dinsa, to taimakonsa ya je yi, domin har amfani ake yi da motocinsa da kuma tufafinsa.
An dakatar da jaruma Samha M Inuwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta dakatar da jaruma Samha M. Inuwa daga Kannywood na tsawon shekara ɗaya.
Hukumar ta dakatar da Samha saboda wallafa hotuna da bidiyoyi da suka sabawa addini da al'adun mutanen Kano wanda hukumar ke adawa da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng