Hadimin Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Yi Murabus, Ya Koma bayan Abokin Hamayyarsa

Hadimin Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Yi Murabus, Ya Koma bayan Abokin Hamayyarsa

  • Daya daga cikin hadiman mataimakin shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Benjamin Kalu, ya yi murabus daga mukaminsa
  • Hadimin ya nuna godiyarsa ga Benjamin Kalu kan damar da ya ba shi ta yin aiki a karkashin ofishinsa, inda ya ce ba zai manta da karamcin ba
  • Sai dai, ya nuna cewa lokaci ya yi da za su raba hanya, inda ya koma goyon bayan mai neman kujerar Benjamin Kalu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Abia - Wani mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya yi murabus daga mukaminsa.

Tsohon hadimin na Benjamin Kalu ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar jam'iyyar LP, Chima Anyaso, gabanin babban zaben shekarar 2027 a jihar Abia.

Hadimin Benjamin Kalu ya yi murabus
Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu Hoto: House of Representatives Federal Republic of Nigeria
Source: Facebook

Ugochukwu Nwankwo ya mika takardar murabus dinsa ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 8 ga Mayu, 2026, amma wadda aka bayyana wa jama'a a ranar Asabar, 4 ga Yuli ta hanyar wani rubutu da Promise Okoro ya yi a Facebook.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya burma matsala da aka bukaci ya biya N50bn

Hadimin Benjamin Kalu ya yi murabus

A cikin wasikar da aka aikawa mataimakin shugaban Majalisar, Mista Nwankwo ya bayyana babban zabe mai zuwa a matsayin dalilin yanke shawararsa.

“Ina so na sanar da kai a hukumance cewa na yi murabus daga mukamina na mataimaki na musamman a gare ka. Wannan shawara ta zama dole domin kauce wa yin ba daidai ba, yayin da muke shirin shiga babban zabe (na 2027)."
“Ina kuma so na yi amfani da wannan dama domin nuna godiyata gare ka bisa ganin cancantata da ka yi na yi maka aiki a wannan matsayi, wani karamci ne da ba na wasa da shi.”

- Ugochukwu Nwankwo

Ya koma goyon bayan abokin hamayya

Mista Okoro, wanda ya wallafa kofin wasikar a dandalin Facebook, ya rubuta cewa:

“Domin bayani gare ku, Mista Nwankwo ya yi murabus a matsayin wanda mataimakin shugaban majalisar ya nada a ranar 8 ga Mayu, 2026.”
"A shekarar 2027, mun yanke shawarar marawa Chima Anyaso baya.”

Kara karanta wannan

Rahoton IMF: Atiku ya aika tambaya ga Tinubu kan 'wanda ke sace 2%' na kuɗaɗen Najeriya

Mista Anyaso shi ne dan takarar jam'iyyar LP na kujerar mazaɓar tarayya ta Bende, wadda Mista Kalu ke zaune a kai a halin yanzu.

Hadimin Benjamin Kalu ya yi murabus
Benjamin Kalu na jawabi a zauren majalisar wakilai Hoto: House of Representatives Federal Republic of Nigeria
Source: Facebook

An tabbatar da murabus din

Jaridar Premium Times ta kira daya daga cikin lambobin tarho da ke kan takardar da aka sanya a dandalin Facebook.

Mutumin da ya amsa kiran ya tabbatar da cewa takardar murabus din sahihiya ce, kuma lallai Mista Nwankwo ya yi murabus daga ofishin Benjamin Kalu. Sai dai mutumin ya ki bayyana ko shi wane ne.

Kalu ya fara zawarcin Alex Otti zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya bukaci Gwamna Alex Otti ya shiga jam'iyyar APC.

Benjamin Kalu ya yi kira a bainar jama’a ga Dr Alex Otti, kan ya fice daga jam’iyyar LP ya koma APC mai mulki a Najeriya.

Mataimakin shugaban majalisar ya ba da tabbacin cikakken goyon baya ga Gwamna Otti idan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng