An Yi Mummunar Guguwa a Sokoto, Gidaje Sun Ruguje, Mutane Sun Mutu

An Yi Mummunar Guguwa a Sokoto, Gidaje Sun Ruguje, Mutane Sun Mutu

  • Mutane huɗu sun rasa rayukansu bayan ruwan sama mai ƙarfi da guguwa sun afkawa wasu al'ummomi a ƙaramar hukumar Kware a Sokoto
  • Daruruwan iyalai sun rasa matsugunansu, yayin da makarantar firamare da asibiti suka samu mummunar ɓarna sakamakon bala'in
  • Rahoto ya nuna cewa hukumar NEMA ta fara tantance irin barnar da aka yi domin kai agajin gaggawa ga waɗanda hadarin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Aƙalla mutum huɗu sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da iska mai ƙarfi da suka afkawa wasu al'ummomi a ƙaramar hukumar Kware ta jihar Sokoto.

Bala'in wanda ya faru a ranar Asabar ya kuma lalata gidaje masu yawa, tare da haddasa ɓarna ga muhimman gine-ginen gwamnati da suka haɗa da makarantar firamare da wani asibiti.

Kara karanta wannan

Matasa 9 sun rasu a hanyar neman arziki daga Sokoto zuwa Legas

Gidajen da suka rushe a Sokoto
NEMA ta isa wajen da guguwa ta rusa gidaje a Sokoto. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa daruruwan iyalai sun rasa matsugunansu bayan gidajensu sun rushe ko kuma suka samu mummunar ɓarna sakamakon guguwar.

NEMA ta fara tantance barnar

Bayan afkuwar lamarin, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ofishinta na ayyuka a Sokoto, ta tura tawagar tantancewa domin gano girman barnar da kuma irin taimakon gaggawar da waɗanda abin ya shafa ke buƙata.

Tawagar ta kai ziyara zuwa ƙauyukan Mallamawa, Mai Mushe, Kaura, Sabon Gari, Rungin Tsamiya da sauran al'ummomin da guguwar ta shafa.

A cewar rahoton farko da NEMA ta wallafa a Facebook, bala'in ya shafi daruruwan gidaje, inda da dama suka rushe gaba ɗaya yayin da wasu suka samu mummunar lalacewa.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa mutane huɗu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.

Mutane sun rasa gidajensu

Rahotonnni sun tabbatar da cewa ɗaruruwan iyalai sun zama marasa matsuguni sakamakon lalacewar gidajensu bayan iska da ruwan da aka yi.

Kara karanta wannan

An yi girgizar kasa sau 2 a jere a Iran, wasu mutane sun jikkata

Haka kuma, wasu muhimman cibiyoyin gwamnati da suka haɗa da makarantar firamare da asibiti sun lalace, lamarin da ka iya shafar ayyukan ilimi da kiwon lafiya a yankunan.

NEMA ta bayyana cewa manufar tantancewar ita ce tattara cikakkun bayanai kan irin barnar da aka yi domin a hanzarta kai kayan agaji da sauran tallafin jin ƙai ga waɗanda abin ya shafa.

Jami'an hukumar NEMA a bakin aiki
Jami'an NEMA a gidajen da suka rushe a Sokoto. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

Hukumar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar Sokoto da hukumomin ƙananan hukumomi domin tabbatar da cewa an kai taimakon da ya dace ga al'ummomin da guguwar ta shafa.

Gidaje sun rushe a Yobe

A wani labarin, mun ruwaito cewa aƙalla mutum uku sun rasa rayukansu bayan ruwan sama mai ƙarfi tare da iska sun afkawa wasu yankuna na ƙaramar hukumar Nguru a jihar Yobe.

Lamarin ya shafi tsohuwar Nguru, Filing Idi da wasu al'ummomin da ke kewaye, inda gidaje da kadarori na miliyoyin naira suka lalace, yayin da daruruwan iyalai suka tsere daga gidajensu.

Wani mazaunin yankin, Bukar Adamu, ya ce bala'in ya faru ne da daddare, inda ya rusa gidaje, katanga da sauran kadarori masu yawa, lamarin da ya tilasta mutane neman mafaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng