EFCC ta yi nasara, kotu ta raba tsohon babban soja da matarsa da dukiyarsu har abada

EFCC ta yi nasara, kotu ta raba tsohon babban soja da matarsa da dukiyarsu har abada

  • Alkalin Babban kotun tarayya mai zama a Abuja ya zartar da hukunci a shari’ar EFCC da AVM Saliu Atawodi (rtd)
  • Kotu ta yarda da lauyoyin hukumar EFCC cewa ta hanyar haram Saliu Atawodi ya mallaki wasu dukiyoyinsa
  • Wannan hukunci da aka zartar ya shafi AVM Atawodi da mai dakinsa da kuma matarsa, Winnie Atawodi

Abuja - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta bada umarni a karbe wasu kadarori da kudin tsohon sojan saman kasar nan, Saliu Atawodi da iyalinsa.

Premium Times ta ce a ranar jiya, 16 ga watan Maris 2022, Alkalin kotun tarayyar ya zartar da wannan hukunci a kan AVM Saliu Atawodi mai ritaya da matarsa.

Kotu ta amincewa EFCC ta karbe kadarori da tsabar dukiya na $200, 000 da wasu Naira miliyan 120 da ake zargin tsohon sojan da matarsa Winnie sun mallaka.

Kara karanta wannan

Bacin zuciya: Kotu ta yankewa malamin addini hukuncin kisa bayan ya kashe amininsa

Hukumar EFCC ta hannun mai magana da yawun bakinta watau Wilson Uwujaren ta tabbatar da wannan hukunci da Alkali Emeke Chikere ya zartar a garin Abuja.

Kamar yadda jawabin da Mista Uwujaren ya fitar a Facebook ya nuna, Mai shari’a Emeka Chikere ya gamsu da zargin cewa ba ta halal aka mallaki wannan dukiya ba.

Saliu Atawodi ya yi asara

Daga cikin dukiyar da aka karbe akwai wani katafaren gini na Atawodi da kamfanin Vector Integrated Services Limited suke amfani da shi a birnin tarayya.

EFCC HQ
Hedikwatar hukumar EFCC Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Kudin da lauyoyin EFCC su ka yi nasarar karbewa na tsohon hafsun sojan saman sun hada da Dala 228,428.16 (kimanin Naira miliyan 120) da N120, 546,042.02.

Alkalin kotun ya dogara ne da dokar manya da sauran makamantan laifuffuka na shekarar 2006.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

EFCC ta gamsar da Emeke Chikere

Mai shari’a Emeke Chikere ya zartar da cewa lauyoyin EFCC sun iya gamsar da shi cewa an saba dokar safarar kudi ta shekarar 2011 wajen mallakar dukiyar nan.

Emeke Chikere ya ce tun da ba a iya kalubalantar hukuncin farko da aka yi na karbe kadarori da kudin ba, ya amince a tattara komai a mikawa gwamnatin tarayya.

Legit.ng ta fahimci an dade ana binciken Air Vice Marshal Atawodi mai ritaya ya taba rike shugaban kwamitin nan na PICOMSS da shugaban kasa ya kafa.

Badakala a NNPC?

Dazu nan aka ji cewa a shekarar 2019, NNPC ta fitar da ganguna sama da miliyan 100 na danyen man fetur a Najeriya, amma babu labarin inda aka kai kudinsu.

Sakamakon binciken da ofishin AuGF ya aikawa Majalisar Tarayya ya nuna ya nemi a tasa darektan NNPC a gaba a kan inda aka kai wasu N663,896,567,227.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Najeriya na fuskantar barazanar asarar sama da Naira Biliyan 1 a kullum

Asali: Legit.ng

Online view pixel