Handame N1.5bn: Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA shekaru 7 a gidan kaso

Handame N1.5bn: Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA shekaru 7 a gidan kaso

- Babbar kotun gwamnatin tarayya mai zama a Lagos ta daure tsohon daraktan NIMASA, Captain Ezekiel Bala Agaba, na tsawon shekaru bakwai a gidan kaso

- A hannu daya kuma kotun ta wanke Government Tompolo, Akpobolokemi tare da wasu mutane 20 da ake zarginsu da hannu a sace makudan kudaden

- A shekarar 2015 hukumar EFCC ta shigar da kara kotun tana zargin wadanda ake tuhumar da sama da fadi da N1.5bn

Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Lagos ta daure tsohon shugaban hukumar gudanarwar tasoshin ruwa da kiyaye hadurra NIMASA, Captain Ezekiel Bala Agaba, na tsawon shekaru bakwai a gidan kaso bayan da aka same shi da almundahanar N1.5bn.

Agaba, wanda ya ke kula da sashen jiragen ruwa, kiyaye hadurra da shige da ficen kaya, an tabbatar da cewa ya sace kudaden daga asusun hukumar.

Mai shari'a Ibrahim Buba ne ya yanke wannan hukunci a ranar Laraba, a yayin da kotun ke ci gaba da sauraren karar da hukumar EFCC ta shigar kan zambar kudin da akayi a hukumar.

A hannu daya kuwa, mai shari'a Ibrahim Buba ya wanke Government Tompolo, tsohon babban darakta janar na hukumar NIMASA, Akpobolokemi tare da wasu mutane 20 da ake zarginsu da hannu a sace makudan kudaden.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2015, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa dukiyar al'umma zagon kasa EFCC ta yi zargin cewa Captain Ezekiel Bala Agaba da ake tuhumar a lokacin da yake mukamin babban darakta a hukumar NIMASA, ya hada baki da tsohon babban shugaban hukumar Patrick Akpobolokemi, domin sace wadannan makudan kudade ta hanyar yin karya da cewa gwamnatin tarayya, lamarin da daga bisani akayi sama da fadi da kudin.

Cikakken rahoton yana zuwa...

KARANTA WANNAN: Harin Borno: Rundunar 'yan sanda ta ceto sojoji 2 daga hannun Boko Haram

Handame N1.5bn: Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA shekaru 7 a gidan kaso
Handame N1.5bn: Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA shekaru 7 a gidan kaso
Asali: Twitter

A wani labarin kuwa, Rundunar 'yan sanda karkashin sashen dakile ta'addanci ta samu nasarar ceto wasu sojoji guda biyu da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su bayan da suka kai wani hari a jihar Borno.

A cikin wani rahoto na 'al'amarin da ke faruwa'. SITREP, da jaridar PRNigeria ta samu, ya bayyana cewa jami'an rundunar 'yan sandan sun yi bata kashi da 'yan ta'addan kafin suka samu nasarar kwato sojojin.

"Da misalin karfe 2:00 na ranar 13 ga watan Yulin 2020, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki wa tawagar tsaro ta rundunar soji akan hanyar Auno, inda suka kashe sojoji biyu tare da sace wasu, yayin da suka yi awon gaba da bindigogi guda biyu kirar AK 47 mallakin sojojin da kuma harsasai masu yawa.

"Sashen dakile ta'addanci na rundunar 'yan sanda sun samu damar gudanar da bin sahun 'yan ta'addan, inda suka yi musayar wuta, a karshe suka kwato bindiga guda daya da harsasai, sannan suka samu nasarar kubutar da sojoji guda biyu da ransu.

"Dukkanin abubuwan da aka kwato an mikasu a hannun hukumar rundunar 'yan sandan," cewar rahoton tsaron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel