An Yi Girgizar Kasa Sau 2 a Jere a Iran, Wasu Mutane Sun Jikkata

An Yi Girgizar Kasa Sau 2 a Jere a Iran, Wasu Mutane Sun Jikkata

  • Mutane uku sun ji rauni sakamakon girgizar ƙasa biyu da suka afku a yankin Kozran da ke jihar Kermanshah a yammacin ƙasar Iran
  • Girgizar ƙasa ta farko mai ƙarfin maki 5.2 ta afku ne da misalin ƙarfe 7:13 na safe, yayin da ta biyu mai ƙarfin maki 5.7 ta biyo baya bayan mintuna biyar
  • Afkuwar wannan al'amari na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙaruwar rikicin soja da musayar hare-hare tsakanin Iran da Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran – Aƙalla mutane uku ne suka samu raunuka sakamakon wata girgizar ƙasa da ta afka wa yankin Kozran da ke jihar Kermanshah a yammacin ƙasar Iran a ranar Litinin, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

Kakakin Hukumar Agajin Gaggawa da Kula da Annoba ta Iran ya bayyana cewa, girgizar ƙasa ta farko mai ƙarfin maki 5.2 a ma'aunin Richter ta auku ne da misalin ƙarfe 7:13 na safe kuma tana da zurfin ƙilomita 8.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Trump ta dauki matakin da zai shafi dalibai da 'yan jaridar Najeriya

Wani waje da aka yi girgizar kasa
Yadda aka yi girgizar kasa a Iran a shekarun baya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An sake girgizar kasa a Iran

Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa Mintuna biyar kacal tsakani, wato da ƙarfe 7:18 na safe, sai kuma wata girgizar ƙasar ta biyu mai ƙarfin maki 5.7 ta sake afkuwa kuma tana da zurfin ƙilomita 13.

Gabanin hakan, shugaban tsarin gudanar da al'amuran gaggawa na Jami'ar Kimiyyar Magunguna ta Kermanshah ya sanar da tura tawagogin tantance halin da ake ciki zuwa tsakiyar yankin da abin ya shafa.

Yawan girgizar kasa a Iran

Wannan al'amari na faruwa ne kwana ƙaɗan bayan da aka ruwaito wata girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 5.0 da ta afkawa yankin Saland na jihar Khuzestan a Kudu maso yammacin ƙasar a jiya Lahadi (19 ga Yulin 2026).

Hukumar Agajin Taimakon Gaggawa ta Red Crescent a Iran ta aike da tawagogin ceto zuwa ƙauyukan yankin domin tantance lalacewar da aka samu.

Rahoton WIO News ya nuna cewa Iran na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fuskantar girgizar ƙasa a duniya saboda yanayin zamanta a tsakiyar daftarin tectonic na Arabian da Eurasian.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan hoton da Messi ke yi wa Yamal wanka a baho

Kodayake yawancin girgizar ƙasa a ƙasar suna kasancewa masu sauki, girgizar da ke afkuwa kusa da saman ƙasa tana da hatsari sosai wajen lalata dukiyoyi.

Mojtaba Khamenei a Iran
Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei da wasu jami'ansa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ssabuwar girgizar ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da tsamin ɗangantaka da hare-hare ke ƙara tsananta tsakanin sojojin Amurka da na Iran, inda ɓangarorin biyu suka shafe mako guda suna musayar hare-hare.

Sojan Amurka ya mutu a Iraq

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani sojan Amurka ya rasa ransa a Arewacin ƙasar Iraki sakamakon fashewar wani bam da bai tashi ba daga wani jirgin Iran da aka harbo.

Hedkwatar sojojin Amurka ta CENTCOM ta bayyana cewa sojan ya rasu ne yayin gudanar da aikin warware makamin da ke ɗauke da bom ɗin da bai tashi ba, inda wani sojan daban kuma ya samu rauni.

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan wani hari da aka kai cibiyar sojojin Amurka a Jordan wanda ya ƙashe sojoji biyu sannan guda ɗaya ya ɓata, yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da kai wa juna hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng