Muhimman Abubauwan Da Ya Kama Ku Sani a Tarihin Rayuwar Peter Obi

Muhimman Abubauwan Da Ya Kama Ku Sani a Tarihin Rayuwar Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, na ɗaya daga cikin waɗanda ake wa hasashen zasu iya samun nasara a zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.

Obi wanda tsohon gwamna ne a jihar Anambra na tsawon zango biyu ya nuna wa duniya zai iya bayan ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa LP a watan Mayu, ana gab da zaɓen fidda gwani.

A wannan zaman, Legit.ng Hausa ta zakulo maku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da rayuwar Peter Obi.

Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Asali: UGC

Haihuwarsa

Cikakken sunansa, Peter Gregory Obi amma ya fi shahara da Peter Obi. An haife shi a ranar 19 ga watan Yuli, 1961 kimanin shekaru 61 kenan da suka gabata a garin Onitsha, jihar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zabe Ya Gabato, Har Yanzu Babban Ministan Buhari Ya Ki Yarda Ya Goyi Bayan Tinubu

Obi sanannen ɗan kasuwa ne saboda ya fito daga iyalin da suka baiwa kasuwanci muhimmanci kafin daga bisani ya shiga aikin banki.

Tarihin karatunsa

Peter Obi ya yi karatunsa na Firamare a mahaifarsa Onitsha jihar Anambra, ya wuce ya kammala karatun Sakandire a Christ the King Collage dake Onitsha.

Daga nan ya shiga jami'ar Najeriya da ke Nsukka, inda ya gama digirinsa na farko a Philosophy a 1984. Bai tsaya iya nan ba, Obi ya yi karatu a kasashen waje da dama.

Ya halarci manyan makarantu a duniya kamar Harvard Business School, London School of Economics, da Columbia Business School da ke New York, a ƙasar Amurka ya karanci kwasa-kwasai.

Ayyukan da ya yi kafin shiga siyasa

Kafin tsoma hannu a siyasa Peter Obi ɗan kasuwa ne, ya rike manyan mukamai a kamfanoni masu zaman kansu da bankunan kasuwanci da dama.

Wuraren da ya yi aiki kafin fara siyasa sun ƙunshi, International Nigeria Ltd, Ciyaman kuma Darakta a Bankin Guardian Express Mortgage, Future View Securities Limited, Paymaster Nigeria Limited, da sauransu.

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 10 da baku sani ba game da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP

Tarihin siyasarsa

Siyasar Obi cike take da kalubale masu rikitarwa. A 2003 ya nemi takarar gwamnan Anambra a inuwar jam'iyyar APGA amma INEC ta ayyana Chris Ngige, na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara.

Bayan shafe kusan shekaru uku ana fafatawa a gaban Kotu, Obi ya samu nasara, inda Alkali ya ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓe kuma aka rantsar da shi ranar 17 ga watan Maris, 2006.

Ya fusakanci kalubale mai girma lokacin da majalisar dokokin Anambra ta tsige shi daga matsayin gwamnan kuma mataimakiyarsa, Virginia Etiba, ta maye gurbinsa ta zama mace ta farko a tarihin Najeriya.

Kotun daukaka kara ta maida shi matsayinsa na gwamna bayan rushe kudirin tsige shi a watan Fabrairu, 2007. Ya nemi tazarce a 2010 inda ya tumurmusa Charles Soludo na PDP watau gwamnan Anambra a yanzu.

Bayan gama zango biyu a matsayin gwamna, Obi ya samu ɗaukaka a matakin siyasar ƙasa inda ake kallonsa da alamar shugabanci na gari bayan ya sauya sheƙa zuwa PDP a 2014.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 11 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Dan Takarar Shugaban Kasa Na NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso

A watan Oktoba, 2018 aka ayyana Peter Obi a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaɓen 2019.

Takarar shugaban ƙasa a 2023

A watan Maris, 2022, Mista Obi ya bayyana kudirinsa na neman takarar shugaban kasa a inuwar PDP amma daga baya ya sauya shawari, ya ce zai nemi takara a Labour Party.

A ruwayar jaridar Premium Times, Obi ya tura wasikar murabus daga zama mamba ga shugabannin PDP. Ya yi zargin saye Deleget da wasu kura-kurai da zagon ƙasa a zaben fidda gwani.

Obidient

Bayan tsayawa takarar shugaban ƙasa a LP, a karon farko Obi ya ja hankalin matasan Najeriya mafi yawa ba su wuce shekara 30 ba zuwa cikin tafiyar Obidient.

Channels tv ta tattaro cewa duk da rashin tsarin LP, Obi da magoya bayansa yan Obidient na ganin lokaci ya yi da tsofaffi zasu kauce su barwa matasa mulkin ƙasar nan.

Masu hasashen kan zaɓen ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023 na ganin tsere ne tsakanin manyan zakunan yan takara uku, Tinubu, Atiku da Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel