Samu lambar NIN dinka: NIMC ta jero cibiyoyi 15,000 na rajistar katin dan kasa a Najeriya

Samu lambar NIN dinka: NIMC ta jero cibiyoyi 15,000 na rajistar katin dan kasa a Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin rufe layukan mutanen da basu lika layukansu da lambobin shaidar kasa ta NIN ba
  • Wannan lamari ya zo da damuwa, kasancewar 'yan Najeriya da dama basu da lambobin NIN balle su lika da layukansu
  • Wata sanarwa da ta fito daga hukumar NIMC, ta bayyana adadin cibiyoyin rajistar NIN da ake dasu a kasar nan da ma kasashen waje

Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC) a ranar Laraba, 6 ga Afrilu, ta sanar da cewa tana da cibiyoyi sama da 15,000 a kasar nan inda ‘yan Najeriya da sauran 'yan kasashen su za su iya yin rajistar lambar shaidar dan kasa ta NIN.

Hukumar ta kara da cewa akwai sama da cibiyoyi 150 a kasashe 40 na waje domin yin wannan rajista ta NIN.

Kara karanta wannan

An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro

Legit.ng ta samo cewa NIMC ta bayyana hakan ne bayan da gwamnatin tarayya ta umurci dukkan kamfanonin sadarwa da su datse kiran wayar duk wadanda ba su lika layukansu da NIN ba.

Hada layuka da NIMC
Mallaki lambar NIN dinka: MINC ta lissafa cibiyoyi 15,000 da ake rajistar katin dan kasa a Najeriya | Hoto: thecable.ng
Asali: Twitter

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun nuna cewa kimanin mutane miliyan 72.77 ke ciki tsundmun a wannan sabon umarnin na gwamnatin tarayya.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce:

“Ya ku ‘yan Najeriya/Mazauna a tsarin shari’a, ana sanar da ke cewa Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC) tana da cibiyoyin rajista sama da dubu goma sha biyar (15,000) na NIN a fadin Jihohi 36 da FCT.
“Akwai cibiyoyi sama da 150 a cikin kasashe 40 na waje. Da fatan za a danna likau dinnan don duba cibiyar rajistar NIN mafi kusa da ku."

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Cikakken jerin cibiyoyin rajista na NIMC

Daga Abia zuwa Zamfara, zaku iya samun jerin cibiyoyin rajista na NIN na duk jihohi 36 da ma FCT, danna nan.

Haka kuma akwai cibiyoyi da dama na yin rajista ga ‘yan Najeriya da ke kasashen waje. Jerin, a cewar NIMC, ana sabunta shi akai-akai.

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta maye gurbin lambobin NIN da wani abun daban

A wani labarin, a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba ne gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na bullo da wata lambar alama da za ta maye gurbin lambobi 11 da ake da su a halin yanzu na NIN.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnati ta ce daga watan Janairun 2022, sabuwar lambar alamar za ta zama madadi ga NIN ga duk 'yan Najeriya a fadin kasar.

A cikin wani dan littafi da Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC) ta fitar, gwamnatin Najeriya ta ce zai zama doka idan aka gano wani kamfani ko hukuma na tabbatar da NIN a ayyukansu.

Kara karanta wannan

ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando

Asali: Legit.ng

Online view pixel