NIN: Layin wayoyin salular sama da mutum miliyan 160 na fuskantar barazana
-Za a iya rufe layin wayoyin mutane kusan miliyan 161.5 saboda rajistar NIN
-Gwamnatin Tarayya ta ce dole a hada kowane layi da lambar NIN din mai ita
-Zai yi wahala a iya yi wa miliyoyin mutane wannan aiki cikin kwana 14 kacal
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa watakila a rufe kusan layin wayoyin salula 161.5 a Najeriya nan da ranar Alhamis, 31 ga watan Disamba, 2020.
Muddin gwamnatin tarayya ba ta kara wa’adin da ta ba kamfanoni ba, dinbin mutane za su samu kansu cikin matsala, za a toshe layukan wayoyinsu.
Ana ganin cewa wa’adin da Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya bada, ya yi kadan a gama hada SIM da NIN.
Binciken da Daily Trust ta yi, ya nuna zai yi matukar wahala mutane kimanin miliyan 160 su kammala wannan aiki nan da kwana 14 (karshen Disamba).
KU KARANTA: Za a rufe duk layin da bai da rajista a bana - NCC
Yanayin wannan aiki da gwamnatin tarayya ta zo da shi ya na da daukar lokaci, sannan kuma masu amfani da wayoyin salula suna da matukar yawa a kasar.
Alkaluman NCC ya nuna masu amfani da wayoyin salula sun karu da 2.2% a Oktoban shekarar bana, hakan ya sa adadin masu rike waya ya kai miliyan 203.5.
A daidai wannan lokaci, hukumar NIMC mai alhakin rajista da bada lambar ‘yan kasa ta iya yi wa mutane miliyan 42 kacal rajista ne a cikin tsawon shekaru 10.
Shakka babu, NIMC da mutum miliyan 40 kadai ta iya yi wa rajista tun 2010 har zuwa bana, ba za ta iya yi wa ragowar mutane miliyan 160 rajista a mako biyu ba.
KU KARANTA: Yadda ake gane ko an yi wa layi rajista
Masana irinsu tsohon shugaban kungiyar kamfanonin sadarwa, Olusola Teniola ya ce zai yi wahala a iya wannan aiki domin ‘yan Najeriya miliyan 28 ba su da NIN.
A baya kun ji yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bada umarnin cewa kowane layi ya zama yana dauke da lambar NIN na mai dauke da layin wayar.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ya ba kamfanonin MTN, GLO, Airtel, 9Mobile da sauransu kwanaki 14 ne su yi wannan jan aiki.
Kawo yanzu wurare 173 ake da su a jihohi 30 da su ke yi wa jama’a rajistar NIMC a fadin kasar nan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng