Shugaba Buhari yaki amincewa da tsarin sabon kudin bai daya na ECOWAS

Shugaba Buhari yaki amincewa da tsarin sabon kudin bai daya na ECOWAS

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace bai yadda da sabon kudurin kudin bai daya da kungiyar ECOWAS ta kawo na yankin yammacin Afrika, a bisa dalilin sa na cewa bai yarda da kasashen na yammacin Afirka ba wanda Faransa ta raina

Shugaba Buhari yaki amincewa da tsarin sabon kudin bai daya na ECOWAS
Shugaba Buhari yaki amincewa da tsarin sabon kudin bai daya na ECOWAS

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace bai yadda da sabon kudurin kudin bai daya da kungiyar ECOWAS ta kawo na yankin yammacin Afrika, a bisa dalilin sa na cewa bai yarda da kasashen na yammacin Afirka ba wanda Faransa ta raina.

DUBA WANNAN: A bisa dukkan alamu dai Dino Melaye zai samu nasara a kiranyen da ake yi masa

Duk da irin murna da maraba da miliyoyin mutane daban-daban bakaken fata na yankin Afirka suke yi akan tsarin fito da sabon kudin na bai daya, wasu manyan shugabanni musamman ma wadanda kasar Ingila ta raina sun nuna rashin amincewar su.

Shugaban Najeriyan Muhammadu Buhari, wanda yaki halartar taron na kasashen yammacin Afirka, wanda aka yi a kasar Ghana, yace yana kokwanto akan wasu kasashe musamman ma kasashen da Faransa ta raina, inda ya bukaci su gabatar da cikakken bayani da zai nuna cewar basu da wata alaka da baitulmalin Faransa din.

Shuganan na Najeriya yace;

"Shugabannin kasashen ECOWAS basu da masaniya akan abubuwan da suka jibanci amfani da kudin bai daya, musamman ma ga wadanda kawo yanzu al'ummarsu basu shirya ba. Saboda haka ina kira ga kasashen da suke amfani da kudin Faransa dasu fito su nuna aniyarsu don su bamu karfin guiwa wajen bada goyon bayan gabatar da kudin na bai-daya. Ya kamata kasashen su gabatar mana da cikakken bayani wanda zai tabbatar mana cewa basu da alaka da baitulmalin Faransa."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng