Naira ta kusa zama labari: Za'a fara amfani da kudin ECO nan da shekara 1 - Ouattara

Naira ta kusa zama labari: Za'a fara amfani da kudin ECO nan da shekara 1 - Ouattara

- Bayan amincewa da fara amfani da kudin bai daya a yankin yammacin Afirka, wanda aka sanyawa kudin suna ECO

- Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya bayyana cewa nan da shekarar 2020 kasashen da suka amince da shirin zasu fara amfani da kudin

- Kasashen sun amince da shirin ne a wannan shekarar, wanda ya samo asali shekaru talatin da suka gabata

Shugaban kasar Ivory Cost Alassane Ouattara ya bayyana cewa kasashen dake yammacin Afirka da suka yadda da sharuddan samar da kudin bai daya wanda aka sanyawa suna ECO za su gabatar da shirin nan da shekara daya mai zuwa.

An fara zancen shirin kudin bai dayan tun shekaru talatin da suka wuce, amma tun lokacin an kasa cimma matsaya akan shirin, saboda banbancin ra'ayi da ake samu tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS.

KU KARANTA: Masha Allah: Mace Bahaushiya da ta fi kowacce mace kyau da kankantar shekaru cikin 'yan siyasar Najeriya (Hotuna)

A watan da ya gabata ne shugabannin su ka amince da shirin, inda Alassane Ouattara ya bayyana cewa kasarsa na goyon bayan shirin dari bisa dari.

Akwai yiwuwar tsarin kudin zai taka muhimmiyar rawa wurin hada kan al'ummar kasashen, sannan kuma shirin zai kawo bunkasar tattalin arziki da samar da aikin yi ga al'ummar kasashen.

A wani taro na kungiyar AU da kasashen Afirka ta yamman suka gabatar a birnin Yamai dake Jamhuriyyar Nijar, sun amince da sanyawa kudin suna ECO, wanda shine zai zama takaddar kudin da ilahirin kasashen Afirka ta yamma za su ke amfani da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel