Abin Tausayi: Yara Ƴan Gida Ɗaya Sun Mutu yayin Dawowa daga Islamiyya a Katsina

Abin Tausayi: Yara Ƴan Gida Ɗaya Sun Mutu yayin Dawowa daga Islamiyya a Katsina

  • Wasu yara 'yan gida daya sun gamu da tsautsayi a jihar Katsina bayan rasa rayukansu sanadiyar ambaliyar ruwa
  • Iyayen yaran da mazauna Janbago sun bayyana bakin cikinsu, suna rokon gwamnatin Katsina ta gina magudanan ruwa
  • Shugabannin al'umma sun ce Janbago na fama da ambaliya sama da shekara goma saboda rashin isassun magudanan ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Janbago, Katsina - An shgia jimami bayan rasuwar wasu yara ƙanana yan gida daya sanadiyyar ambaliayar ruwa.

Yaran 'yan uwan juna biyu, Muhammad Salisu mai shekara 12 da Abdurrahman Salisu mai shekara 7, sun rasa rayukansu a unguwar Janbago da ke Katsina.

Yan gida daya sun mutu sanadiyar ambaliyar ruwa a Katsina
Taswirar jihar Katsina da aka samu ambliyar ruwa a wani yanki. Hoto: Legit.
Source: Original

Yara sun mutu sanadiyar ambaliyar ruwa

Rahotanni sun ce yaran na kan hanyarsu ta komawa gida daga wata makarantar Islamiyya da ke kusa lokacin da ruwan sama mai karfi tare da iska ya mamaye tituna, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaɓen 2027, gwamna Caleb ya nemi afuwar ƴan ƙabilar Igbo kan yakin basasa

Bayan dogon bincike da mazauna yankin suka gudanar, an gano gawarwakin yaran a wurare daban-daban, lamarin da ya jefa daukacin al'ummar Janbago cikin alhini.

Mutane da dama sun taru a gidan iyayen yaran domin yi musu ta'aziyya da jajanta musu kan wannan babban rashi da ya girgiza al'ummar yankin.

Mahaifin yaran, Malam Salisu Arabi, cikin hawaye ya ce wannan shi ne mafi tsananin bakin ciki da ya taba fuskanta a rayuwarsa.

Ya ce yaran sun fita makarantar Islamiyya kamar yadda suka saba, amma bai taba tunanin cewa ruwan saman ranar zai kwace masa 'ya'yansa biyu ba.

Malam Salisu ya yi addu'ar Allah Ya gafarta musu Ya kuma ba su Aljannatul Firdaus, tare da rokon gwamnati ta dauki matakan hana sake faruwar irin wannan bala'i.

Mahaifiyar yaran, wadda ta kasa boye damuwarta, ta ce ba za ta taba manta da 'ya'yanta ba, domin su ne farin cikinta da babban fatanta.

An bukaci Gwamna Radda ya kawo dauki kan ambaliyar ruwa
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina. Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Musabbabin faruwar ambaliyar ruwan

Mazauna yankin sun bayyana cewa ana iya kauce wa wannan ibtila'i, suna zargin matsalar ta samo asali ne daga rashin isassun magudanan ruwa a Janbago.

Kara karanta wannan

Matukan tankar mai sun ruga da gudu a Hormuz yayin da Iran ke barin wuta

Wani dattijo ya ce duk lokacin da aka yi ruwan sama mai yawa, ruwa daga sassa daban-daban na karamar hukumar Katsina kan taru a Janbago.

A cewarsa, al'umma sun sha rubuta koke tare da rokon gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa su samar da magudanan ruwa, amma har yanzu babu cikakken mafita.

Shugaban Kungiyar Raya Al'ummar Janbago, Malam Tajuddeen, ya ce matsalar ambaliyar ta shafe sama da shekara goma tana hana ci gaban yankin, cewar Daily Post.

Ya bayyana cewa wannan na daga cikin mafi munin abubuwan da suka faru saboda ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar yara da ba su san komai ba.

Tajudden ya roki Gwamna Dikko Umaru Radda da ya kawo dauki cikin gaggawa, yana mai cewa matsalar ta zama barazana ga rayuka ba wai muhalli kadai ba.

Mazauna yankin sun bukaci gwamnatin Katsina da hukumomin da abin ya shafa su gaggauta gina ingantattun magudanan ruwa da ayyukan dakile ambaliya kafin sake afkuwar wata irin wannan masifa.

Za a yi ambaliya a Kaduna, wasu jihohi

Kun ji cewa hukumar NIHSA ta gargadi jihohi 17 da su shirya saboda yiwuwar ambaliya daga ranar 21 zuwa 27 ga Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Ricikin bayan zaben fitar da gwan ya raba kan APC a jihar Niger

Bauchi, Edo, Imo, Kaduna, Plateau da Benue na cikin jihohin da aka ce za su fuskanci matsakaicin hadarin ambaliya a mako guda.

NIHSA ta bukaci jama'a su kaurace wa yankunan da ke kusa da koguna tare da guje wa ketare hanyoyin da ruwa ya mamaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.