Kai Tsaye: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasar 2023

Kai Tsaye: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasar 2023

A yau Laraba, 6 ga Satumba, 2023, za a yanke hukunci a kan karar shugaban kasa da 'yan takaran PDP, LP da APM su ka shigar.

Atiku Abubakar da Peter Obi ba su yarda da nasarar da Bola Tinubu ya samu ba, su na kalubalantar jam'iyyar APC da INEC a kotu.

Za a haska zaman kotun a gidajen talabijin kasar nan, kuma an ji cewa ba a bukatar ganin kowa sai wadanda aka tantance shi.

Za mu rika kawo rahoto kai-tsaye a kan yadda abubuwa su ke faruwa a kotun na Abuja.

Bola Tinubu ya ji dadin samun nasara

A rahoton NTA, an ji Mai girma shugaban kasa ya yi farin ciki da hukuncin da kotu ta zartar na ba shi nasara a kan abokan adawarsa a zaben 2023.

Bola Tinubu ya jinjinawa alkalan sannan ya yi kira da abokan hamayyarsa su taimaka wajen kawo cigaba tun da ta tabbata shi ya lashe zabe.

Daga karshe kotun zabe ta yi watsi da ƙararrakin Atiku da Obi, ta tabbatar da Tinubu

Biyo bayan karanta hujjojin da kowane ɓangare ya gabatar, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar.

Kotun ta tabbatar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Kotu ta yi watsi da shaidu 15 cikin 27 da Atiku ya gabatar

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta yi watsi da hujjojin da shaidu 15 cikin 27 da Atiku ya gabatar a gabanta.

Mai shari'a Stephen Adah, wanda ɗaya ne daga cikin alkalai biyar da ke yanke hukunci a kotun ne ya bayyana hakan kamar yadda The Punch ta wallafa.

Kotun ta ce Atiku ya gaza shigar da shaidun na sa da kuma hujjojinsu a lokacin da ya shigar da ƙorafe-ƙorafensa a gabanta.

An baza jami'an tsaro a Abuja

Tun a yammacin Talata aka samu labari motocin ‘yan sanda sun shiga sintiri a lunguna da sakonnin birnin Abuja.

Jami'an tsaro na 'yan sanda, NSCDC da masu fararen kaya sun shiryawa zaman kotun shari’ar zaben 2023 da za ayi.

Kotu ta yi watsa-watsa da Lauyoyin Atiku

Daily Trust ta ce kotun zabe ta yi watsi da ikirarin Lauyoyin Atiku Abubakar na cewa Bola Tinubu ya na da katin zama ‘dan kasar Guinea.

Moses Ugo ta kuma yi fatali da zargin cewa hukumomin Amurka sun karbe $460, 000 daga hannun Bola Tinubu saboda harkar kwayoyi.

Mai shari’ar ta ce ‘dan takaran na PDP ya shigo da sababbin batutuwa ne wanda ba su da hurumi a doka.

Kotun zabe ta gama da korafe-korafen Peter Obi, ta shiga cikin na Atiku Abubakar

Kotun zabe ta kammala karanto korafe-korafen Peter Obi, waɗanda ta yi watsi da mafi yawa daga cikinsu.

Yanzu kuma kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta dukufa cikin korafe-korafen da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya shigar.

Makomar Tinubu ta na ga Lauyoyin Atiku

Rahoton The Cable ya ce tun da an yi watsi da kararrakin LP da 'dan takararta, yanzu an dogara ne da karfin hujjojin lauyoyin PDP.

Tun farko aka soke karar APM, abin da zai taba kujerar Bola Tinubu shi ne samun nasarar Atiku Abubakar a kotun karar zaben.

Kotu ta ce shari’ar da aka yi da Bola Tinubu a Amurka bai nufin ya yi laifi ko ya shiga gidan yari ko ya yi harkar miyagun kwayoyi.

Dokar zabe bata yi tanadi kan tura sakamakon zabe ta na’ura ba – Kotun zabe

Kotun zaben shugaban kasa ta ce dokar zabe ta 2022 ba ta yi tanadi kan tura sakamakon zabe ta na’ura ba.

Kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani, ya ce na’ura daya tilo da aka wajabtawa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) amfani da ita wajen gudanar da zaben, ita ce BVAS.

Duk a kan batun kin bin dokar zabe da ka’idojin INEC, Kotun zaben ce babu wani abu a cikin dokar da ke nuna dole sai na’urar BVAS ta tura sakamakon rumfunan zabe, Channels TV ta rahoto.

Kotun ta kuma bayyana cewa, shafin duba sakamakon hukumar (IReV) ba wajen tattara sakamako ba ne, kuma hukuncin da aka yanke na Oyetola da INEC ya goyi bayan hakan a fili.

Kotu ta yi watsi da bukatar dole INEC ta tura sakamakon zaben ta na'urar BVAS

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da korafin rashin aika sakamakon zabe ta na'urar BVAS.

Jam'iyyar Labour na korafin cewa hukumar INEC ba ta aika dukkan sakamakon zabe ta na'urar ba.

Mai Shari'a Haruna Tsammani ya ce ba dole ne sai ta aika sakamakon ba, INEC tana da hurumin yin hakan, amma bai zama tilas ba.

Kotu ta yi watsi da korafin LP da Obi kan kuri'un Abuja

Kotun zabe ta yi watsi da karar jam'iyyar LP da Obi na cewa mutum na bukatar samun kaso 25 cikin dari na kuri’un yan Abuja kafin ya lashe zaben shugaban kasa.

A cewar kotun, mazauna babban birnin tarayya basu da wata dama ta musamman kamar yadda masu karar suka yi ikirari, Channels TV ta rahoto.

Peter Obi v Bola Tinubu

Kotu ta ce shari’ar da aka yi da Bola Tinubu a Amurka a shekarun baya bai nufin ya aikata laifi ko ya shiga gidan yari saboda badakalar miyagun kwayoyi.

Kotu ta yi watsi da hujjojin shaidu 10 cikin 13 da Peter Obi ya gabatar

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yi watsi da hujjojin da shaidu 10 cikin 13 da Peter Obi ya gabatar, waɗanda ta ce ba gamsassu ba ne.

Mai shari'a Haruna Tsammani ya sanar da yin watsi da hujjojin shaidun 10 da jam'iyyar Labour da Peter Obi suka gabatar kamar yadda AIT ta ruwaito.

Kotu ta fara sauraran karar Atiku Abubakar

Kotu ta kira bangaren dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar don gabatar da kara.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP, Umar Damagun ya na wakiltar Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP.

Chris Uche shi ne babban lauyan da ke kare Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP.

Kotu na ci gaba da sauraran korafi daga bangaren Peter Obi

Kotun ta ce duk da Peter Obi da jam'iyyar Labour sun bayyana cewa sun samu halastattun kuri'u kuma mafi yawa, sun gagara kawo yawan kuri'un.

Kotun ta ce abin da ake dubawa a zabe shi ne yawan kuri'u.

Alkalai sun yi hukunci cewa jam'iyyar hamayya ba ta iya nuna rumfunan zaben da aka yi magudi ba, saboda haka The Cable ta ce aka soke batun.

Mai shari'a Haruna Tsammani ya yi watsi da wasu ikirarin da Peter Obi yake yi

Kotu na karanta korafe-korafen Peter Obi

Bayan dawowa daga hutun daƙiƙu 15, kotu ta ci gaba da karanto korafe-korafen Peter Obi na jam'iyyar Labour.

Alkalai sun iso kotu

Tashar Channels ta rahoto lokacin da Alkalai su ka shirya domin fara gabatar da hukunci a shari'ar da ake ta jiran tsammani.

Kotu ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar APM ta shigar a kan Tinubu da Shettima

Bayan karanta ƙorafe-ƙorafen da jam'iyyar APM ta shigar, inda ta nemi kotu ta soke zaɓen Tinubu saboda rashin cancanta, mai shari'a Haruna Tsammani ya kori ƙarar ta APM.

Ya kori ƙarar ne saboda rashin cancantuwar shigar da ita kamar yadda AIT ta ruwaito.

Tuni aka fara zaman kotun sauraran kararrakin zabe

A halin yanzu zama ya yi nisa don sanin sahihin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Tuni aka fara zaman sauraran kararrakin zaben a kotun da ke birnin Tarayyar Nigeria, Abuja.

An fara ne da ƙorafe-ƙorafen da jam'iyyar APM ta shigar tana neman a soke nasara Shugaba Tinubu.

Lauyoyi sun fara neman wurin zama a kotu

A halin yanzu, lauyoyi sun hallara a kotu tare da shirya neman wurin zama don ci gaba da sauraran kararrakin zaben shugaban kasa.

Ganduje, Gwamnan Bauchi da Abdullahi Sule sun hallara a kotun zabe

An hangi shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje, Sanata Bala Mohammed na Bauchi, da kuma Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a cikin kotun zaɓen.

Haka nan duk a cikin kotun, Julius Abure na jam'iyyar Labour ma ya samu hallara.

AIT ta ce mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro, Nuhu Ribadu da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila su na cikin kotun.

Haka zalika an ga fuskokin gwamnonin APC na Yobe, Ekiti, Imo da kuma Kogi.

Kashim Shettima ya hallara a kotun kararrakin zabe

A halin da ake ciki, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya isa kotun sauraran kararrakin zaben da ke birnin Abuja.

Yayin da Kashim Shettima ya isa kotun, Bola Tinubu ya tafi taron G20 a Indiya.

Idan baku manta ba, a yau ne ake karasa zaman domin sanin makomar nasarar Bola Ahmad Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Online view pixel