Amurka Ta Gano Tarkon da Isra'ila Ta Kafa Mata a Warware Yaki da Iran

Amurka Ta Gano Tarkon da Isra'ila Ta Kafa Mata a Warware Yaki da Iran

  • Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance ya zargi wasu mambobin gwamnatin Isra'ila da ƙoƙarin sauya ra'ayin Amurkawa kan Iran
  • JD Vance ya bayyana cewa an tura maƙudan kuɗi a asirce don kawo cikas ga tattaunawar yarjejeniyar sulhu da ƙasar Iran a Gabas ta Tsakiya
  • Fadar White House ta amsa cewa lallai wasu ƙasashen waje suna ƙoƙarin yin tasiri a kan ra'ayin al'ummar Amurka ke bayyanawa a kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mataimakin Shugaban Ƙasar Amurka, JD Vance, ya zargi wasu mambobin gwamnatin Isra'ila da ƙoƙarin yin tasiri ga ra'ayin al'ummar Amurka domin tsawaita yaƙin da ake yi da Iran.

A cikin wata hira da aka wallafa a ranar Laraba, Vance ya shaida cewa ko da yake yana amincewa da wasu mutane a gwamnatin Isra'ila, akwai wasu masu juya tunanin Amurkawa don ganin yaƙin ya ci gaba har abada.

Kara karanta wannan

Bauchi: Bala Mohammed ya yi garambawul a majalisar zartarwa, ya sauke kwamishinoni 2

JD Vance da Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu a hagu da JD Vance a dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

BBC ta wallafa cewa fadar White House, ta bakin sakatariyar yaɗa labaranta Karoline Leavitt, ta bayyana a ranar Alhamis cewa Shugaban Amurka ya amince cewa ƙasashen waje na ƙoƙarin yin tasiri ga ra'ayin jama'ar ƙasar.

Amurka ta zargi kasar Isra'ila

Yayin da yake jawabi a shirin The Joe Rogan Experience, Vance ya bayyana cewa mutane a cikin gwamnatin Isra'ila sun yi ƙoƙarin kauce wa yarjejeniyar sulhu da Iran.

Ya ce akwai hujjoji na zahiri da ke nuna cewa wasu shugabannin Isra'ila "sun tsani yarjejeniyar," kuma sun gudanar da kamfe na asirce mai ɗauke da maƙudan kuɗi don kawo cikas ga tattaunawar.

A watan da ya gabata ne Amurka ta cimma yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da Iran, wadda ta haɗa da tsagaita wuta na kwanaki 60 da kuma sake buɗe Hormuz, ko da yake an sake samun takaddama a baya-bayan nan.

Damuwar mataimakin shugaban ƙasa

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: INEC na shirin yin zaben gwaji kafin siyasar 2027 a Najeriya

Vance, wanda ya taka rawar gani a tattaunawar sulhun ta hanyar ziyartar Pakistan a watan Afrilu da Switzerland a watan Yunin 2026, ya ce ba ya damuwa idan wasu ɓangarori a Isra'ila sun soki matsayar Amurka.

Yahoo News ta wallafa cewa ya ce:

"Abin da ke damuna shi ne lokacin da shugabannin Amurka suka bar wannan lamari ya shafi tunaninsu da kuma matsayar da suke karewa,"
Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump zai tafi kasar China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar tallafawa Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa 'yan jam'iyyar Democrats a majalisar wakilan Amurka sun rarrabu sosai a ranar Laraba yayin kaɗa ƙuri'a kan batun dakatar da tallafin soja ga ƙasar Isra'ila.

Kusan rabin mambobin jam'iyyar Democrats ne suka goyi bayan matakin rage ko yanke tallafin, lamarin da ya nuna rarrabuwar kai tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar da kuma mambobinta.

Yayin da wasu ke kiran da a dakatar da taimakon har sai Isra'ila ta sauya dabarunta a Gaza, shugabannin jam'iyyar kamar Hakeem Jeffries sun kaɗa ƙuri'ar ƙiyayya ga matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng