Yadda Legas da Wasu Jihohi 5 Suka Raba Naira Tiriliyan 3.79 daga Asusun FAAC
- Jihohin Kudu maso Yamma shida sun karɓi Naira tiriliyan 3.79 daga rabon asusun FAAC tsakanin 2023 da rubu'in farko na 2026
- Jihar Legas ce ta samu kaso mai tsoka a kudin, inda ta karbi Naira tiriliyan 1.44, yayin da Oyo ta zo ta biyu da Naira biliyan 635.62
- Ana sa ran jihohin su yi amfani da kuɗaɗen wajen biyan albashi, gina ababen more rayuwa da gudanar da ayyukan gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Legas - Jihohi shida na yankin Kudu maso Yamma sun karɓi jimillar Naira tiriliyan 3.79 daga rabon kuɗaɗen asusun FAAC tsakanin shekarar 2023 da rubu'in farko na shekarar 2026.
FAAC ce ke rarraba kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ta tara ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi domin gudanar da ayyukansu na kundin tsarin mulki.

Source: Twitter
Legas ta fi karɓar kuɗin FAAC a yankin
Binciken rabon kuɗaɗen cikin watanni 39 ya nuna cewa Legas ce ta fi karɓar kuɗi, inda ta samu jimillar Naira tiriliyan 1.44, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.
A matsayi na biyu akwai Oyo da ta karɓi Naira biliyan 635.62, sai Ondo da Naira biliyan 550.08.
Sauran sun haɗa da Osun da ta samu Naira biliyan 423.7, Ogun da Naira biliyan 372.4, da Ekiti wadda ta karɓi Naira biliyan 366.92.
Yadda jihohin suka karɓi kuɗin a kowace shekara
1. Legas
Legas ta samu Naira biliyan 371.39 a shekarar 2023, Naira biliyan 368.93 a 2024, sannan kuɗin ya haura zuwa Naira biliyan 514.6 a 2025. A watanni ukun farko na 2026 kuma ta karɓi Naira biliyan 184.9.
2. Oyo
Oyo ta samu Naira biliyan 207.37 a 2023, Naira biliyan 145.25 a 2024, Naira biliyan 213.7 a 2025, sannan Naira biliyan 69.3 a rubu'in farko na 2026.
3. Ondo
Ondo ta karɓi Naira biliyan 156.33 a 2023, Naira biliyan 142.45 a 2024, Naira biliyan 198.4 a 2025, da Naira biliyan 52.9 a watanni ukun farko na 2026.
4. Osun
Osun ta samu Naira biliyan 141.48 a 2023, Naira biliyan 97.21 a 2024, Naira biliyan 144.9 a 2025, sannan Naira biliyan 40.1 a rubu'in farko na 2026.

Source: UGC
5. Ekiti
Ekiti ta karɓi Naira biliyan 107.5 a 2023, Naira biliyan 93.22 a 2024, Naira biliyan 130.3 a 2025, da Naira biliyan 35.9 a farkon 2026.
6. Ogun
Ogun kuwa ta samu Naira biliyan 120.72 a 2023, Naira biliyan 90.77 a 2024, Naira biliyan 124.2 a 2025, sannan Naira biliyan 36.7 tsakanin Janairu da Maris na 2026.
Ana sa ran jihohin su yi amfani da kuɗaɗen FAAC wajen biyan albashi da fansho, gina da gyaran hanyoyi, inganta harkokin lafiya da ilimi, tallafa wa tsaro, bunƙasa noma da aiwatar da sauran ayyukan raya ƙasa domin amfanin al'umma.
Gwamnati na karkakatar da kudin FAAC?
A wani labari, mun ruwaito cewa, ma'aikatar kuɗi ta ƙasa ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa ana karkatar da kuɗaɗen shigar gwamnati ko ana kashe kudin a ɓoye ba gaskiya ba ne.
Cire kuɗaɗe daga asusun FAAC ba ɓata kuɗi ba ne, face biyan buƙatun doka kamar tsaro, da kuma maido wa jihohi haƙƙoƙinsu, cewar Taiwo Oyedele.
Gwamnatin tarayya ta kuma soki yadda wasu ke amfani da tsofaffin bayanai da watsi da sauye-sauyen da aka samu a farkon 2026 don sukar gwamnati.
Asali: Legit.ng


