Tinubu Zai Yi Magana gaban Shugabannin Kasashen Duniya a Amurka, An Sanya Lokaci

Tinubu Zai Yi Magana gaban Shugabannin Kasashen Duniya a Amurka, An Sanya Lokaci

  • Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na 81, inda zai gabatar da jawabi ga shugabannin kasashe
  • Tinubu zai tattauna kan tsaron iyakokin Yammacin Afirka, makamashi, ilimi, lafiya, da bayyana sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa
  • Jakadan Najeriya ya ce akwai yiwuwar Tinubu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a gefen taron da za a gudanar a watan Satumba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA), wanda za a fara a birnin New York na Amurka a watan Satumba.

Babban jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa a ranar Laraba.

Shugaba Bola Tinubu zai yi magana a taron majalisar dinkin duniya na UNGA a Amurka.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na jawabi a babban taron UNGA karo na 78. Hoto: ANGELA WEISS/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Tinubu zai halarci taron majalisar dinkin duniya

Kara karanta wannan

Kallo ya koma kan Najeriya, Tinubu zai zauna kusa da Trump a Amurka

Ya ce Tinubu ya tabbatar masa da cewa zai halarci taron bayan an gabatar masa da kasafin kudin halartar Najeriya a zaman bana, a cewar rahoton The Cable.

Jimoh Ibrahim ya ce shugaban kasar zai halarci wasu tarurrukan gefen babban taron da za su mayar da hankali kan batutuwan makamashi, ilimi da inganta tsarin gudanar da asibitoci.

A cewarsa, halartar taron zai bai wa Najeriya damar bayyana sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ga kasashen duniya.

Tinubu ya halarci zama na 78 na Majalisar Dinkin Duniya da kansa, yayin da mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilce shi a zama na 79 da na 80.

Najeriya za ta nemi hadin kai kan tsaron iyakoki

Jakadan ya ce Tinubu zai yi amfani da dandalin Majalisar Dinkin Duniya wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yadda za a inganta tsaron iyakokin Yammacin Afirka.

Ya bayyana iyakokin yankin da ba su da cikakken tsaro a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya, yana mai cewa gwamnatin tarayya na hada gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya kan wani shiri na kula da tsaron iyakoki.

Kara karanta wannan

'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya

Ya kara da cewa Najeriya za ta nemi karin goyon bayan kasashen duniya domin tabbatar da nasarar wannan shiri.

Jimoh Ibrahim ya ce Tinubu ya tabbatar masa cewa zai halarci taron UNGA na bana da kansa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (hagu) da babban jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim (dama). Hoto: @JimohIbrahimCFR
Source: Twitter

Ana sa ran Tinubu ya gana da Trump

Jaridar Punch ta rahoto cewa Jimoh Ibrahim ya kuma ce akwai yiwuwar Shugaba Tinubu ya gana da shugaban Amurka, Donald Trump, a gefen taron.

A cewarsa, ana sa ran shugaban Najeriya zai zauna a sahun gaba tare da gabatar da jawabi ga Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya da misalin karfe 10:45 na safe agogon New York.

Za a bude zama na 81 na Majalisar Dinkin Duniya ranar 8 ga watan Satumba, yayin da muhawarar manyan shugabanni za ta gudana daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumba, 2026.

Taron na bana zai hada shugabannin kasashe, gwamnoni da ministoci domin tattauna batutuwan sauyin yanayi, ci gaba mai dorewa, zaman lafiya da tsaro a duniya.

Shettima ya yi magana a UNGA

A wani labari, mun ruwaito cewa, Najeriya ta goyi bayan kiraye-kirayen da Birtaniya, Faransa da wasu kasashe ke yi na kafa kasar Falasdinawa a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Akpabio ya kare dangantakar majalisa da Tinubu, ya fadi dalili

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana matsayar Najeriya a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a Amurka.

Sanata Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce kafa kasar Falasdinu za ta kawo karshen rikicin Falasdinawa da Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com