Gwamnoni 6 Sun Shirya zuwa Wurin Bola Tinubu kan Tikitin Musulmi da Musulmi a Zaben 2027
- Gwamna Babagana Zulum ya gode wa Shugaba Bola Tinubu kan sake tsayar da Kashim Shettima takarar mataimakin shugaban kasa
- Shugaba Tinubu ya amince da bukatar tawagar gwamnonin Arewa maso Gabas ta kai masa ziyarar godiya a fadarsa da ke Abuja
- Gwamna Zulum ya ce wannan ne karon farko da dan asalin Borno ya sake samun tikitin mataimakin shugaban kasa a karo na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa sake tsayar da Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.
Gwamna Zulum ya bayyana matakin a matsayin babban abin alfahari ga jihar Borno da daukacin Arewacin Najeriya.

Source: Twitter
Farfesa Zulum ya kai ziyarar godiya
The Nation ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja
Farfesa Zulum ya ce ya kai ziyarar ne domin isar da godiyar al'ummar Borno tare da neman izinin shugaban kasa na kai masa ziyarar godiya a hukumance.
Gwamnoni 6 za su ziyarci Tinubu
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya amince da bukatar, wanda hakan zai bai wa gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas su shida damar jagorantar tawagar yankin zuwa fadar shugaban kasa a mako mai zuwa.
Zulum ya ce:
"Na zo ne domin gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda sake tsayar da daya daga cikin 'ya'yanmu, Sanata Kashim Shettima, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.
"Haka kuma na nemi izininsa domin daukacin wakilan Arewa maso Gabas su zo su yi masa godiya, kuma cikin sa'a shugaban kasa ya amince."
"Abin tarihi ne ga Borno"
Gwamnan ya ce ziyarar za ta bai wa shugabanni da al'ummar Arewa maso Gabas damar nuna godiyarsu ga shugaban kasa bisa amincewar da ya sake yi wa Shettima.
Ya bayyana sake tsayar da mataimakin shugaban kasar a matsayin wani babban tarihi a siyasar jihar Borno, yana mai cewa wannan ne karon farko da dan asalin jihar ya samu tikitin mataimakin shugaban kasa sau biyu a jere.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Lokacin da Tinubu ya mika wa Shettima fom din zama abokin takararsa a 2027

Source: Facebook
Ya tuna da Babagana Kingibe
Zulum ya tuna cewa a baya irin wannan dama ta kusa samuwa ga Ambasada Babagana Kingibe, sai dai hakan bai tabbata ba, kamar yadda Leadership ta kawo.
Ya kara da cewa:
"Mun yi matukar farin ciki, kuma muna gode wa Allah. Amma mun san wannan matsayi ba na jihar Borno kadai ba ne, na daukacin Arewacin Najeriya ne.
"A madadin al'ummar Arewa, ina gode wa kowa da ya karbi danmu, sannan ina mika godiya ta musamman ga Shugaba Tinubu."
Tinubu ya mikawa Shettima fam
A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya mika wa Kashim Shettima takardar tabbatar da shi a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.
An bayyana lamarin ne cikin wani bidiyo da Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Kafafen Sada Zumunta, Olusegun Dada, ya wallafa a shafinsa
Wannan mataki ya zo ne kwanaki kadan bayan jam'iyyar APC ta tabbatar da Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng
