'Fulani Makiyaya' Sun Yi Barazanar Kashe Malamin Addini da Mabiyansa a Filato

'Fulani Makiyaya' Sun Yi Barazanar Kashe Malamin Addini da Mabiyansa a Filato

  • Fasto Ezekiel Dachomo ya ce ya karbi wasikar barazanar kisa daga wasu da ake zargin 'yan ta'adda bayan kashe 'yan uwansa tara a Filato
  • Malamin ya ce ya mika kwafen wasikar ga jami'an tsaro, yana mai jaddada cewa ba ya tsoron barazanar saboda ya dogara ga Allah
  • Dachomo ya bukaci kasashen duniya su tuna da marayu da zawarawa tare da neman adalci ga wadanda aka kashe a hare-haren Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Filato - Shugaban yankin Cocin Church of Christ in Nations (COCIN), Rev. Ezekiel Dachomo, ya ce wasu da ake zargin 'yan ta'adda sun aika masa da wasikar barazanar kisa.

Rev. Ezekiel Dachomo ya ce an yi masa barazanar ne kwanaki kadan bayan kashe mutum tara daga cikin 'yan uwansa a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Fasto ya yi zargin cewa Fulani Makiyaya sun yi barazanar kashe shi da mabiyansa
Taswirar jihar Sokoto, inda aka yi barazanar kashe wani fasto. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi barazakar kashe fasto

Dachomo ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a, inda ya ce ya mika kwafen wasikar ga jami'an tsaro domin daukar matakin da ya dace.

A cewarsa, an rubuta wasikar da harshen Hausa da Turanci, kuma ta kunshi gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kai masa hari tare da kashe shi.

Dachomo ya ce wadanda suka aiko da wasikar sun yi alkawarin kashe shi kamar yadda suka kashe mutum tara daga cikin danginsa.

Ya bayyana cewa tuni ya mika kwafen wasikun ga jami'an tsaro domin bincike da daukar matakan kariya.

Sai dai ya ce duk da irin wannan barazana, ba ya jin tsoro saboda ya yi imanin cewa rayuwarsa tana hannun Allah Madaukakin Sarki.

An kashe 'yan uwan faston a hari

Malamin cocin ya ce harin da aka kai ya bar masa raunuka masu zafi saboda ya yi jana'izar mutanen da yake kauna tare da jajanta wa iyalan da suka rasa 'yan uwansu.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ƴan sanda sun cafke mayakan Lakurawa da ke addabar garuruwan Arewa

Dachomo ya yi zargin cewa mutum tara daga cikin danginsa na cikin wadanda aka kashe a harin da aka kai garuruwan K'um da Wereng-Camp da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Filato a ranar 11 ga watan Yuli.

Ya ce ya san yadda ake jin radadin binne masoya, da share hawayen yara da suka ga an kashe iyayensu, da kuma ta'azantar da iyalan da suka shiga cikin alhini.

A cewarsa, yanzu ana yi masa barazana cewa shi ne zai zama na gaba, abin da ya sa yake tambayar laifin da ya aikata.

Fasto ya ce ba zai gajiya da kare hakkin zawarawa, marayu da kiristocin Filato ba.
Rev. Ezekiel Dachomo da aka yi barazanar kashe shi a cikin mutanensa a Filato. Hoto: @ezekieldachomo0
Source: Twitter

Fasto ya dage kan akidarsa

Dachomo ya tambaya ko kare hakkin zawarawa, marayu da Kiristocin da ake gallazawa ya zama laifi. Ya ce idan wannan ne laifinsa, zai ci gaba da yin hakan har zuwa numfashinsa na karshe.

Malamin ya kara da cewa ko da za a kashe shi, ba za a iya kashe gaskiyar da yake fada ba, domin a cewarsa za a iya kashe mai isar da sako amma ba za a kashe sakon ba.

'Yan bindiga sun sace fasto da mabiyansa

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sake yin aika-aika a jihar Benue bayan da suka yi garkuwa da wani fasto da ke jagorantar wani coci.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rikata 'yan Boko Haram a kananan hukumomin Borno 5

Hatsabiban 'yan bindigan sun sace faston ne tare da wasu mambobin cocinsa bayan sun kai harin da ya sake jefa mutane cikin firgici.

An mika kokon bara ga jama'a da su yi addu'o'i domin ganin mutanen da aka sace sun kubuta daga hannun 'yan bindiga cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com