Cikakken Jerin Jami'an Tsaron da Suka Sadaukar da Ransu wajen Ceto Dalibai a Oyo

Cikakken Jerin Jami'an Tsaron da Suka Sadaukar da Ransu wajen Ceto Dalibai a Oyo

  • Majalisar Dattawa ta bayyana sunayen jami'an tsaro da suka rasa rayukansu yayin aikin ceto dalibai da malamai da aka sace a jihar Oyo
  • Aikin ya kawo ƙarshen kwanaki 56 da waɗanda aka sace suka shafe a hannun 'yan ta'adda, inda aka ceto yawancinsu cikin nasara
  • Sojoji da 'yan sanda uku sun mutu, wani soja kuma ya jikkata yayin da aka kama mutane takwas da ake zargi da ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - An bayyana sunayen jami'an tsaro da suka sadaukar da rayukansu yayin aikin soji da ya kawo ƙarshen kwanaki 56 da dalibai da malamai da 'yan ta'adda suka sace a ƙaramar hukumar Oriire da ke jihar Oyo.

Bayyanar sunayen ta sake fito da irin sadaukarwar da jami'an tsaron suka yi wajen ceto waɗanda aka sace, duk da cewa aikin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu jami'ai da kuma jikkatar wani soja.

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan ta'addan ISIS ya shigo Najeriya, sojoji sun yi caraf da shi

An rasa jami'an tsaro yayin ceto dalibai a Oyo
Shugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Majalisar Dattawa ce ta bayyana sunayen jami'an yayin da take karrama su saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an ceto waɗanda aka sace.

Sai dai duk da wannan rashi, an samu nasarar ceto mafi yawan dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su, tare da cafke waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Sunayen jami'an da suka rasa rayukansu

Jami'an tsaron da suka mutu yayin wannan aiki sun haɗa da:

  • Laftanar F. A. Isaac na rundunar sojojin Najeriya
  • Private Silas Musa na Bataliya ta 81 ta rundunar sojojin Najeriya
  • Sajan Abena John Jerome na rundunar 'yan sandan Najeriya

Haka kuma, Lance Corporal Adamu Hussain na Bataliya ta 81 ya samu raunuka a musayar wuta, amma ya tsira bayan an yi masa magani.

Yadda aikin ceto ya gudana

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce an fara aikin ne bisa sahihan bayanan sirri bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su tattara dukkanin kayan aiki da ƙarfin da ake da su domin tabbatar da an sako waɗanda aka sace ba tare da wani sharaɗi ba.

Kara karanta wannan

An cafke mata da yaran 'yan bindiga, an saki bidiyo bayan sace daliban Oyo

A cewar Opeyemi Bamidele, aikin ya ɗauki fiye da kwanaki 50 kafin ya kai ga nasarar ceto dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su.

Ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun kama mutane takwas da ake zargi da hannu a satar mutanen, tare da kashe wasu daga cikin 'yan ta'addar yayin aikin, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Sai dai ya bayyana alhininsa kan mutuwar ɗaya daga cikin malaman da aka sace, wanda ya rasu tun yana hannun 'yan ta'addan kafin a kammala aikin ceto.

An ceto dalibai da malamai a Oyo
Taswirar jihar Oyo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Fadar shugaban kasa ta soki Gwamna Makinde

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta caccaki gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, kan kiran da ya yi a gudanar da bincike karkashin Majalisar Dinkin Duniya (UN) game da sace dalibai da malamai a jihar.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kiran da kalaman gwamnan abu ne wanda bai kamata ba, inda ta ce yana kokarin sanya siyasa a lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng