Yadda Siyasar 2027 Ta Kawo Tsaiko kan ’Yancin Kananan Hukumomi a Najeriya

Yadda Siyasar 2027 Ta Kawo Tsaiko kan ’Yancin Kananan Hukumomi a Najeriya

  • Shirye-shiryen siyasar zaɓen 2027 na neman kawo tsaiko a shirin aiwatar da cikakken 'yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi
  • Kungiyar NULGE ta zargi gwamnati da rashin ƙudurin aiwatar da hukuncin, tare da neman a hukunta Akanta Janar
  • An ce yawancin jihohi na ci gaba da amfani da asusun haɗaka, yayin da Jigawa ta fara karɓar kuɗin ƙananan hukumomi kai tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shekaru kusan biyu bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan 'yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi, har yanzu ba a aiwatar da tsarin a yawancin jihohin Najeriya ba.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan ƙananan hukumomi har yanzu suna karɓar kasonsu ta hannun gwamnatocin jihohi maimakon kai tsaye daga Asusun Tarayya.

Har yanzu 'yancin kananan hukumomi bai samu ba
Gwamnonin Najeriya yayin ganawa da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Dalilan jinkiri kan 'yancin kananan hukumomi

Majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa da jam'iyyar APC sun ce siyasar zaɓen shekarar 2027 na daga cikin dalilan jinkirin aiwatar da tsarin, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yawan kujerun sanatoci da APC, PDP ke da su a majalisa bayan zaben cike gurbi

Sun ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya son ɗaukar matakin da zai iya janyo saɓani tsakaninsa da gwamnoni masu muhimmanci ga yaƙin neman zaɓensa.

A watan Yulin 2024, Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin bai wa dukkan ƙananan hukumomi 774 cikakken 'yancin gudanar da harkokinsu da kuɗaɗensu.

Kotun ta bayyana cewa ya saɓa wa kundin tsarin mulki gwamnoni su riƙe ko su rarraba kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi.

Gwamnatin Tarayya ce ta kai ƙarar gwamnoni 36 tana zarginsu da riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi ta hanyar asusun haɗaka na jihohi.

Wani babban jami'in Fadar Shugaban Ƙasa ya ce batun ya zama mai sarkakiya saboda hankalin 'yan siyasa ya koma zaɓen 2027.

Ya ce gwamnati na la'akari da tasirin da matakin zai yi kan dangantakarta da gwamnoni da ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa a zaɓen shugaban ƙasa.

Ana zargin Tinubu na da hannu kan rashin ba kananan hukumomi yancinsu
Shugaba Bola Tinubu yayin wani taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: AFP

Zargin da NULGE ke yi wa gwamnati

Ƙungiyar Ma'aikatan Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, NULGE, ta zargi gwamnati da rashin ƙudurin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.

Sakataren NULGE na ƙasa, Isah Gambo, ya ce babu wata ƙaramar hukuma da ta fara karɓar kuɗinta kai tsaye daga Asusun Tarayya.

Kara karanta wannan

Rigima ta taso a APC bayan sauya 'yan takara, 'yan jam'iyya sun fara tutsu

Ya ce duk da umarnin shugaban ƙasa, jami'an da ke da alhakin aiwatar da tsarin sun ƙi yin hakan ba tare da fuskantar hukunci ba.

Bincike ya nuna mafi yawan jihohi har yanzu na ci gaba da amfani da asusun haɗaka tsakanin jiha da ƙananan hukumomi, cewar Daily Post.

Jami'ai daga Kano, Plateau, Kaduna da Ogun sun ce har yanzu gwamnoninsu ne ke da iko kan yadda ake kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

A Jigawa kuwa, shugaban ALGON na jihar, Sibu Abdullahi, ya ce dukkan ƙananan hukumomi 27 sun fara karɓar kuɗinsu kai tsaye.

Ya ce sabon tsarin ya ba ƙananan hukumomi damar tsara ayyukansu da kansu tare da ƙara gaskiya wajen gudanar da kuɗaɗe.

Kaduna: An musanta kwace kudin kananan hukumomi

Kun ji cewa wani rahoto ya yi yawo mai zargin cewa Gwamna Uba Sani ya kwace kudaden kananan hukumomi inda yake tsakura masu wani kaso dan kadan.

Rahoton ya nuna cewa abin da gwamnan yake tsakurawa kananan hukumomin bai wuce N25m a kowane wata.

Kungiyar shugabannin kananan hukumomi Najeriya (ALGON) reshen jihar Kaduna ta fito ta yi martani kan rahoton wanda aka yada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.