A Karon Farko, Tinubu Zai Tafi Kasar Amurka Don Halartar Babban Taro a Birnin New York

A Karon Farko, Tinubu Zai Tafi Kasar Amurka Don Halartar Babban Taro a Birnin New York

  • A karon farko, Shugaba Tinubu zai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) a birnin New York na Amurka
  • Tinubu zai bar kasar Najeriya ne a ranar Lahadi 17 ga watan Satumba zuwa babban taron da za a yi na kwanaki biyar
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasar ya dawo daga kasar Indiya bayan halartar taro da shugabbannin kasashen duniya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai cilla birnin New York na Amurka a ranar Lahadi 17 ga watan Satumba, Legit ta tattaro.

Tinubu zai halarci Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 78 da za a gudanar a ranar 19 zuwa 23 ga watan Satumba wanda zai zama shi ne karon farko na halartar shugaban.

Kara karanta wannan

Babu Wani Uzuri, Zan Yaki Manyan Matsalolin Najeriya Har Abada - Shugaba Tinubu

Tinubu zai tafi birnin New yORK na Amurka
Tinubu Zai Tafi Kasar Amurka Halartar Babban Taro. Hoto: @OfficialABAT.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu zai tafi taron Amurka?

Shugaban zai gabatar da lakca a ranar Talata 19 ga watan Satumba kafin muhawara da sauran shugabannin duniya da ya shafi harkokin ci gaba mai dorewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, Tinubu zai yi jawabi kan matsalolin da su ka shafi ci gaba mai dorewa da sauyin yanayi da hadin kan duniya da bambance-bambance da ake samu tsakanin mutane.

Zai kuma gana da manyan shugannin duniya kamar na kasashen Brazil da Afirka ta Kudu da shugaban Tarayyar Turai (EU) da sauransu.

Su waye za su raka Tinubu taron a Amurka?

Daga cikin wadanda za su raka Tinubu akwai Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom da na Kogi, Yahaya Bello da na jihar Imo, Hope Uzodinma.

Sauran sun hada da gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani da na Kwara, AbdulRahman AbdulRazak da kuma Seyi Makinda na jihar Oyo, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dawowarsa Ke Da Wuya, Tinubu Ya Sake Nada Babban Mukami, An Bayyana Sunanta

Sannan akwai ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar da shugaban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila sai kuma ministan tattalin arziki da kudade, Wale Edun da sauran ministoci.

Shugaban Amurka, Joe Biden ya Jinjinawa Tinubu a Indiya

A wani labarin, Shugaban Amurka, Joe Biden ya tofa albarkacin bakinsa game da yadda Bola Ahmed Tinubu ya ke jagorantar Najeriya da kuma kungiyar ECOWAS.

A wani jawabi da ya fito daga fadar shugaban Amurka, an ji Joe Biden ya na yabawa irin kokarin da takwaransa na Najeriya yake yi tun da ya dare karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel