'Yan ta'adda na da masu kai musu bayanan sirri a cikin jami'an tsaro, Shugaban NSCDC

'Yan ta'adda na da masu kai musu bayanan sirri a cikin jami'an tsaro, Shugaban NSCDC

  • Shugaban hukumar NSCDC, Dr Ahmed Audi ya ce akwai masu kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a cikin jami'an tsaro
  • Dr Audi ya ce ba daga cikin jami'an tsaro kadai ba, a cikin jama'a akwai masu kai musu rahotannin sirri
  • Shugaban ya bukaci hukumomin tsaro da su sauya salo wurin bai wa kadarorin gwamnati kariya duba da asarar da ake tafkawa duk shekara

Abuja - Babban kwamandan hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), Dakta Ahmed Audi, ya ce wasu daga cikin jami'an tsaro ne ke kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri.

Daily Trust ta ruwaito cewa, babban kwamandan ya sanar da hakan ne yayin wani taro kan bai wa kadarorin kasa kariya da kuma ababen more rayuwa a dakin taro na NAF da ke Abuja a ranar Talata.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

'Yan ta'adda na da masu kai musu bayanan sirri a cikin jami'an tsaro, Shugaban NSCDC
'Yan ta'adda na da masu kai musu bayanan sirri a cikin jami'an tsaro, Shugaban NSCDC. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC
"Za ku yadda da ni cewa miyagun ayyukan 'yan ta'addan nan suna samun karfafawa ne ba daga masu kai musu bayanan sirri a cikin jami'an tsaro ba, har da na cikin jama'a.
"A don haka ne akwai bukatar saka shugabannin gargajiya, na addinai, jama'a, 'yan siyasa da shugabannin matasa wurin shawo kan wannan matsalar," yace.

Audi ya ce hauhawan ta'addanci ya kasance babbar barazana ga manyan kadarorin kasa da ababen more rayuwa inda ya yi misali da jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, Borno da sauran jihohin arewa.

Ya kara da jaddada bukatar sake sabbin tsare-tsare ga hukumomin tsaro wurin bai wa kadarorin kasa kariya daga miyagu masu son tada zaune tsaye.

Babban kwamandan wanda ya nuna damuwarsa kan takardar da ministan yada labarai, Lai Mohammed ya fitar inda ya ce gwamnatin tarayya ta na kashe naira biliyan sittin a kowacce shekara domin gyaran bututun man fetur a kasar nan da aka lalata.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Hakan yasa ya sake magana kan bukatar sake sabbin tsare-tsare domin bai wa kadarorin kasar nan kariya daga 'yan ta'dda, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kaduna: Miyagu sun sheke mutum 8 a farmakin martani da suka kai Zangon Kataf

A wani labarina daban, a wani harin mayar da martani, wasu mutane da ba a san ko su waye ba a kauyen Kacecere da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna sun halaka rayuka takwas, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, a wata takarda da ya fitar, ya ce wannan harin mayar da martani ne wanda aka fara a kauyen Jankasa da ke karamar hukumar Zangon Kataf inda aka kashe wani Yakubu Danjuma tare da halaka wasu mutum 34 da ke Madamai a karamar hukumar Kaura ta jihar.

"Farmakin da aka kai wuraren nan biyu, jami'an tsaro sun gano cewa shi ya janyo farmakin mayar da martani da wasu suka kai yankin Kacecere wanda ya bar rayuka takwas a mace, mutum shida da raunika da kuma gidaje da aka kone," Aruwan yace.

Read also

Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, ciki har da ƙanin ango da matarsa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel