Najeriya Ta Fusata, Ta Kakaba wa Kamfanin Jiragen Saudiyya Tarar Naira Miliyan 6
- Hukumar NCAA ta ci kamfanin jiragen saman Saudiyya tarar N6m saboda take haƙƙin fasinjoji da kuma kasa bin umarnin da aka ba shi
- NCAA ta ce kamfanin ya gaza warware korafe-korafen fasinjoji duk da karin lokaci da aka ba shi domin cika ka'idojin kariyar masu tafiya
- Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da kare haƙƙin fasinjoji tare da hukunta duk kamfanonin jiragen da suka karya dokokin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta kakaba wa kamfanin jirgin sama na Saudi Airlines tarar Naira miliyan shida bisa zargin saba dokokin kare fasinjoji.
Daraktan hulda da jama’a na NCAA, Michael Achimugu, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya ce matakin ya biyo bayan gazawar kamfanin wajen magance wasu matsalolin fasinjoji da aka gabatar masa.

Kara karanta wannan
Musulmai na cikin wani yanayi da aka fara yunkurin haramta kiran Sallah a Denmark

Source: Twitter
Matsalar da kamfanin jirgin Saudiyya ya fuskanta
Achimugu ya ce NCAA ta dade tana bai wa Saudi Airlines damar warware korafe-korafen da fasinjoji suka shigar tare da bin umarnin hukumar, amma kamfanin bai cika bukatun ba, in ji rahoton Premium Times.
Ya bayyana cewa hukumar ta taba shiga tsakani a wani lamari da ya faru a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, wanda ya so rikidewa zuwa rikici.
A cewarsa, hukumar NCAA ta kuma bai wa kamfanin karin lokaci domin ya gyara matsalolin da suka shafi fasinjoji, amma hakan bai yiwu ba.
Najeriya ta yi aiki da doka wajen daukar mataki
Hukumar ta ce ta kakaba wannan hukunci ne bisa tanadin Sashe na 19 na Dokokin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Najeriya (Nig. CARs) 2023, wanda ya tanadi hakkokin fasinjoji da kuma nauyin da ya rataya kan kamfanonin jiragen sama.

Kara karanta wannan
Kano ta yi zarra, ta fi dukkan jihohin Najeriya sababbin masu rijistar katin zaɓe
Achimugu ya ce:
“Babu shakka NCAA ta ci Saudi Airlines tarar Naira miliyan shida saboda laifuffukan da suka shafi kare fasinjoji.”
Hukumar ta bayyana cewa tana fatan wannan hukunci zai sa kamfanin Saudi Airlines ya kara inganta ayyukanta a Najeriya tare da bai wa fasinjoji kulawar da ta dace.
Achimugu ya jaddada cewa dukkan fasinjojin da ke tafiya zuwa ko daga Najeriya suna da hakkin a kula da su cikin adalci da mutunci daga dukkan kamfanonin jiragen sama.

Source: Getty Images
Saudi Airlines ba ta mayar da martani ba
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kamfanin Saudi Airlines bai fitar da wani bayani kan tarar da NCAA ta kakaba masa ba, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Wannan matakin ya zo ne bayan hukumar ta sha gargadin kamfanonin jiragen sama da su guji karya dokokin kare masu amfani.
A watan Satumban 2025, NCAA ta gargadi kamfanonin Royal Air Maroc da Saudi Airlines kan wasu kura-kurai, tana mai cewa za su iya fuskantar hukunci mai tsauri idan ba su bi umarnin hukumar ba.
Jirgi dauke da fasinoji ya samu matsala
A wani labari, mun ruwaito cewa, fasinjojin da suka taso daga Legas zuwa Fatakwal sun shiga fargaba bayan da aka sauya alkiblar jirgin samansu sakamakon matsalar inji.
Kamfanin jirgin Arik ya tabbatar da cewa jirginsa ya sauka a filin jirgin saman Fatakwal da ke Omagwa kafin samun matsalar.
Shugaban sashen hulda da jama’a na kamfanin, Adebanji Ola, ya nemi afuwar fasinjojin da lamarin ya shafa, yana mai jaddada cewa tsaron fasinjoji ne mafi muhimmanci a gare su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
