Gwamnatin Kebbi Ta Shirya Gudanar da Auren Gata, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana
- Gwamnatin Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris, za ta aurar da wasu daga cikin mutanen jihar
- Shirin na auren gata da gwamnatin ta ɓullo da shi, zai amfani mutim 600 da suka haɗa da angwaye 300 da amare 300
- Shugaban kwamitin shirye-shirye, Suleiman Argungu ya bayyana cewa kafin ɗaura aure, sai an gudanar da bincike da gwaje-gwaje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamnatin Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta fara shirye-shiryen gudanar da auren gata a jihar.
Gwamnatin za ta gudanar da auren gatan ne ga mutane 600, waɗanda suka haɗa da anguna 300 da amare 300 a ranar 27 ga watan Fabrairun 2025.

Asali: Facebook
Gwamnatin Kebbi za ta yi auren gata
Shugaban kwamitin shirye-shirye, Alhaji Suleiman Argungu, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi a Birnin Kebbi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa ana gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar wata ƙungiya mai zaman kanta, watau Nafisa Nasir Charity Development Foundation (NANAS).
Za a yi gwaje-gwaje da binciken aure
Ya bayyana cewa an kafa kwamitoci daban-daban domin gudanar da wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da gwaje-gwajen lafiya, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Ya ce gwaje-gwajen da za a yi akwai gwajin ciki, gwajin jini domin tantance genotype da gwajin cutar HIV/AIDS.
Haka nan kuma, za a tantance matsayin aiki ko sana’ar ango domin tabbatar da cewa yana da damar da zai kula da matarsa bayan aure.
Su wanene za su ci gajiyar shirin auren?
Alhaji Suleiman Argungu ya bayyana cewa shirin na auren gata, zai mayar da hankali ne kan marayu, zawarawa, da mutanen da ke da buƙatu na musamman, ba tare da la’akari da ƙabilarsu ko addininsu ba.
Ya ƙara da cewa shirin, cika alƙawari ne da Gwamna Nasir Idris ya yi yayin da aka gudanar da auren gata a baya, inda ya sha alwashin cewa za a riƙa gudanar da shi lokaci zuwa lokaci domin tallafawa marasa hali su samu su yi aure.
Gwamnatin jihar za ta bayar da N180,000 a matsayin sadaki ga kowacce amarya daga cikin amare 300 da aka zaɓo a faɗin ƙananan hukumomi 21 na jihar.
Hakan na nufin gwamnatin za ta kashe jimillar N54m a kan kuɗin sadakin da za a ba amaren.
Baya ga haka, gwamnati za ta samar da kayan daki da kayan abinci ga ma’auratan domin ƙarfafa rayuwar aurensu.
Gwamnatin Kebbi ta kawo tsarin ilmi kyauta
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta kawo tsarin ba da ilmi kyauta ga ɗaliban jihar.
Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa ilmi ya zama kyauta a jihar domin gwamnati ce ke ɗaukar nauyin rajistar jarabawa da kuɗin makarantar ɗalibai.
Hakazalika, gwamnan ya nuna cewa gwamnatinsa na ba da tallafin karatu ga ɗaliban makarantun sakandare da na gaba da sakandare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng