Shiri Ya Yi: Fursunoni 61 Suka Haddace Al Kur'ani Mai Girma a Kano

Shiri Ya Yi: Fursunoni 61 Suka Haddace Al Kur'ani Mai Girma a Kano

  • Fursunoni 61 a gidan gyaran hali da ke Kurmawa a jihar Kano sun kammala haddar Alƙur’ani mai girma
  • Maza 55 da mata shida ne suka yi nasarar kammala haddace Al-kur'ani mai girma a gidan gyaran halin da ke Kano
  • An ba su tallafin kayan masarufi da kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwar komawa cikin al'umma bayan sun kammala zamansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Fursunoni 61 da ke zaman hukuncin ɗauri a gidan gyaran hali da ke Kurmawa a jihar Kano sun yi nasarar kammala karatun da haddar Alƙur’ani mai girma.

Waɗanda suka kammala haddar Al-kur'anin mai girma a gidan gyaran halin sun haɗa da maza 55 da mata shida.

Fursunoni sun haddace Al-kur'ani a gida gyara hali a Kano
Fursunonin da suka sauke Al-Kur'ani a Kano Hoto: Nigerian Correctional Service
Source: Facebook

Kakakin hukumar hula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCoS) reshen jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano wasu ƴan ta'addan ƙasashen waje a Borno, sun karya lagon ISWAP

Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya ce fursunonin sun nuna ƙwazo da juriya matuƙa a tsawon lokacin gudanar da shirin.

Yadda fursunonin suka haddace Alƙur’ani

Kofar Nasarawa ya sanar da cewa da yawa ​daga cikin fursunonin ba su da gogewa kan karatun Alƙur’ani kafin shigarsu gidan gyaran hali.

Sai dai ya ce ta hanyar mayar da hankali, jajircewa da kuma koyarwar addini, fursunonin sun samu nasarar haddace Alƙur’ani gaba ɗaya.

Kakakin ya ƙara da cewa wannan nasara ta nuna irin tasirin shirye-shiryen gyaran hali da suka ginu a kan koyarwar addini.

A cewarsa, hakan kuma ya tabbatar da ƙudirin hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya na gyarawa, horaswa da sake haɗa fursunoni cikin al'umma daidai da tanade-tanaden dokar hukumar gyaran hali ta Najeriya ta shekarar 2019.

An ba waɗanda suka kammala shirin tallafi

Domin karrama waɗanda suka kammala shirin, hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya tare da haɗin gwiwar wata ƙungiya mai zaman kanta sun ba kowane ɗaya daga cikinsu tallafin kayayyaki.

Tallafin ya haɗa da sababbin kaya, katifu, barguna da kuma kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da kyautata rayuwarsu da kuma sauƙaƙa musu komawa cikin al'umma bayan kammala zamansu a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

'Sai Arewa ta yi tsayin daka': Inuwa Yahaya ya zaburar da gwamnoni a Kaduna

Shugabanni sun yabawa shirin

Kakakin ya ce Kwanturolan hukumar kula da gidajen gyaran hali na jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yaba da jagorancin Babban Kwanturolan Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche.

Ya ce jagorancin Nwakuche ya taimaka wajen bunƙasa shirye-shiryen ilimi, koyon sana'o'i da tarbiyya a cibiyoyin gyaran hali a faɗin ƙasar.

Lakpene ya bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na bai wa fursunoni ilimi, ƙwarewa da kyawawan ɗabi'u da za su taimaka musu su zama masu amfani ga al'umma bayan an sake su.

Fursunoni sun haddace Al kur'ani a Kano
Fursunoni mata da suka sauke Al-kur'ani a Kano Hoto: Nigerian Correctional Service
Source: Facebook

A nata ɓangaren, shugabar kwamitin afuwa na jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta sake jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na inganta walwalar fursunoni.

Ta kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa tausayinsa da ci gaba da tallafa wa fursunoni a cibiyoyin gyaran hali da ke faɗin jihar.

Hakimin Kawaji kuma Dan Ruwatan Kano, Alhaji Ibrahim Ado Bayero, ne ya miƙa takardun shaidar kammala shirin ga fursunoni 61 a yayin bikin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Sokoto, an kashe mutane da jikkata wasu

Fursunoni sun tsere daga gidan yari

A wani labarin kuma, kun ji cewa fursunoni 12 sun sere daga gidan gyaran hali da tarbiyya na tarayya da ke Kotonkarfe a jihar Kogi.

Gwamnatin jihar Kogi tare da hukumomin tsaro sun sha alwashin cewa za su dauki matakan hana afkuwar irin hakan a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng