Qatar Ta Ware Kwanakin Makoki, Ta ba da Hutun Aiki bayan Mutuwar Tsohon Sarki
- Qatar ta ayyana zaman makoki na kwanaki hudu bayan rasuwar tsohon Sarkin ƙasar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, wanda ya rasu yana da shekara 74.
- Gwamnati ta dakatar da aiki a ma'aikatu da hukumomin gwamnati, tare da umartar a sauke tutocin ƙasa rabin sanda domin girmama marigayin.
- Sheikh Hamad ya jagoranci Qatar daga 1995 zuwa 2013, inda ya sauya ƙasar zuwa babbar cibiyar tattalin arziki kafin ya mika mulki ga ɗansa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Doha, Qatar - Kasar Qatar ta ayyana zaman makoki na ƙasa na tsawon kwanaki huɗu bayan rasuwar tsohon Sarkin ƙasar wanda ya tayar da hankali.
Marigayin wanda mahaifin Sarkin kasar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya rasu yana da shekara 74 a duniya.

Source: Getty Images
An sanar da zaman makoki a Qatar
Fadar Masarautar Qatar ta sanar da cewa zaman makokin ya fara ne daga ranar Lahadi, 12 ga Yulin 2026, cewar Times of India.
A wannan lokaci, za a sauke tutocin ƙasar zuwa rabin sanda domin girmama tsohon shugaban.
A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen makoki, gwamnati ta dakatar da aiki a ma'aikatu, hukumomin gwamnati da cibiyoyin gwamnati daga Litinin, 13 ga Yuli. Ma'aikata za su koma bakin aiki ranar Lahadi, 19 ga Yuli.
Sheikh Hamad ya jagoranci Qatar daga shekarar 1995 zuwa 2013. Ana yabawa jagorancinsa saboda sauya Qatar zuwa ɗaya daga cikin manyan ƙasashen tattalin arziki da tasiri a yanki da ma duniya.

Source: Getty Images
Gudunmawar da marigayin ya bayar a Qatar
A cikin shekaru 18 da ya yi yana mulki, ya jagoranci manyan ayyukan gine-gine, bunƙasa tattalin arziki da sauye-sauyen da suka ƙarfafa matsayin Qatar a idon duniya.
A zamaninsa, Qatar ta amince da kundin tsarin mulkinta na dindindin a shekarar 2004. Haka kuma an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi tare da bai wa mata damar kaɗa ƙuri'a da neman muƙami.
Mulkinsa ya kuma yi daidai da manyan tarukan duniya, ciki har da Wasannin Asiya na 2006 a Doha, taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na 2012, da yarjejeniyoyin Doha.
A shekarar 2013, Sheikh Hamad ya mika mulki da kansa ga ɗansa, Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani wanda har yanzu yake ci gaba da jagorantar kasar.
Hakan ya sa ya kasance cikin kaɗan daga cikin sarakunan ƙasashen Larabawa da suka sauka daga mulki da son rai suna raye domin ba magajinsu dama.
Sarkin Qatar ya yi waya da Donald Trump
A baya, kun ji cewa Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya yi magana da Shugaba Donald Trump ta wayar salula kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Fadar Sarkin Qatar ta tabbatar da tattaunawar shugabannin kasashen biyu, inda ta jero muhimman batutuwan da suka tabo musamman game da Gabas ta Tsakiya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sake shirya tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a karo na biyu a birnin Islamabad.
Asali: Legit.ng

