Buhari zai kaddamar da yaki da yin 'fitsari da kashi' barkatai

Buhari zai kaddamar da yaki da yin 'fitsari da kashi' barkatai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da yaki da yin 'kashi da fitsari' barkatai a fadin Najeriya.

An saka wa yaki da 'fitsari da kashi' a bainar jama'a suna 'domin tsaftace Najeriya, yi amfani da bandaki (Clean Nigeria, Use Toilet)', sai dai ba a sanar da lokacin da shugaban kasa zai kaddamar da hakan ba.

Yin hakan na daga cikin kokarin gwamnati na kawo karshen yaki da yin 'fitsari da kashi' a fili zuwa karshen shekarar 2025.

A kalla mutane miliyan 47 ne ke yin bahaya a filin Allah a Najeriya, kamar yadda bincike ya nuna. Kananan hukumomi 10 ne kacal daga cikin 774 dake Najeriya aka bayyana a matsayin wadanda ba a yin bahaya a fili a yayin da Buhari ya kaddamar da shirin tsaftar muhalla.

Buhari zai kaddamar da yaki da yin 'fitsari da kashi' barkatai
Buhari
Asali: Facebook

Ministan albarkatun ruwa na kasa, Sulaiman Adamu, ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron kwamitin zartar wa na gwamnatin tarayya, wanda aka yi a fadar shugaban kasa dake Abuja.

"Mun dauki wasu matakai domin tabbatar da tsaftar muhalli yayin tattaunawar mu kafin ranar da shugaba Buhari zai kaddamar da yaki da yin bahaya a fili, wanda aka yiwa lakabi da 'domin tsaftace Najeriya, yi amfani da bandaki'

DUBA WANNAN: Kisa da kona gidaje: Hotunan barnar da mayakan Boko Haram suka tafka a Molai

"Shugaban kasa da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa zasu kasance wakilan tabbatar da tsaftace muhalli a fadin Najeriya da kuma tabbatar da samun nasarar shirin da shugaban kasa zai kaddamar.

"Mun nemi kudi N10.6 domin tabbatar da nasarar shirin, ba iya gwamnati ce kadai zata samar da kudaden ba, kungiyoyi daa kamfanoni zasu bayar da gudunmawar kudin da za a yi amfani da su wajen yin amfani da jaruman fim, matasa, yara da mata wajen wayar da kan jama'a a kan illolin yin bahaya a fili da muhimmancin tsaftar muhalli," a kalaman ministan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel