An Shiga Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Daliban Jami'ar Tarayya a Nasarawa

An Shiga Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Daliban Jami'ar Tarayya a Nasarawa

  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga sun kutsa masaukin daliban Jami'ar Tarayya ta Lafia da ke jihar Nasarawa, sun sace dalibai uku
  • Rundunar 'yan sandan Nasarawa ta kaddamar da samame domin ceto daliban da aka sace tare da cafke wadanda suka kai harin
  • Anc e 'yan sanda sun ceto dalibi daya yayin da rundunar ta gargadi dalibai su guji zama a wuraren da ke cikin daji saboda hadarin hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Nasarawa - Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sace dalibai uku na Jami'ar Tarayya ta Lafia (FULafia) daga gidan da suke zama da ke wajen jami'ar.

An ce 'yan ta'addar sun farmaki gidan kwanan daliban ne da ke a kan titin Awe, kusa da matsugunnin jami'ar na wucin gadi da ke Akunza a Lafia, jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

An bankado wurare masu hadari a Abuja, an kama mutum 560 da bindigogi

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar Lafia.
Kofar shiga jami'ar tarayya ta Lafia da ke jihar Nasarawa. Hoto: @MySchoolGist
Source: Twitter

'Yan bindiga sun sace daliban jami'a

Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya ce an samu kiran neman dauki da misalin karfe 9:21 na dare, bayan wasu 'yan bindiga sun kai farmaki gidan daliban, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, maharan sun fara balle kofar gidan kafin daga bisani su kutsa ciki tare da sace daliban.

Nansel ya bayyana cewa gidan kwanan daliban yana wani kebantaccen wuri ne kusa da matsugunnin wucin gadi na jami'ar, kuma yana makwabtaka da wata hanya da ta nufi garin Awe.

Ya ce wannan yanayi ne da masu garkuwa da mutane ke amfani da shi wajen tserewa bayan sun aikata laifinsu.

An ceto dalibi 1 daga cikin 3 da aka sace

Sai dai ya ce jami'an tsaro sun yi gaggawar isa wurin bayan samun rahoton lamarin, lamarin da ya kai ga ceto daya daga cikin daliban da aka sace.

Nansel ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, ya umarci tura jami'an musamman da masu sintiri domin gudanar da aikin ceto a cikin dazukan da ke kewaye da yankin.

Kara karanta wannan

Majalisa na neman taka wa Tinubu birki kan tubabbun yan ta'adda a Najeriya

Ya kara da cewa an umarci dukkan bangarorin bincike da na ayyukan rundunar su ci gaba da samamen har sai an ceto sauran daliban biyu ba tare da sun samu rauni ba, tare da kamo wadanda suka aikata laifin.

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar Lafia, jihar Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa, inda 'yan bindiga suka sace daliban jami'ar Lafia. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun gargadi dalibai

Kakakin rundunar ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane kan bi layin wutar lantarki da hanyoyin da shanu ke bi domin shiga daji bayan sun sace mutane.

Saboda haka, ya bukaci dalibai su guji hayar gidaje a wuraren da ke nesa da jama'a saboda arha, yana mai ba su shawarar su hada kai wajen karbar gida a wuraren da suka fi tsaro.

Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna yankin da duk wanda ke da wani bayani mai amfani ya tuntubi jami'an tsaro domin taimakawa wajen ceto sauran daliban da kuma cafke masu garkuwa da mutanen.

'Yan bindiga sun sace dalibai

A wani labari, mun ruwaito cewa, ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai a hanyar zuwa zana jarabawar JAMB, lamarin da ya figita iyaye da 'yan uwansu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tabbatar da cewa jami'an rundunar suna cikin daji domin ceto daliban da aka sace a hanyar zuwa zana jarabawar.

Mazauna yankin sun nuna matukar damuwa kan yadda wannan hanyar ta zama matattarar ’yan bindiga masu addabar matafiya da sace dalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com