Seyi Tinubu da Ƴaƴan Manyan Ƴan Siyasa 4 a Najeriya da Ke Taya Mahaifansu Faɗa
- Tun bayan hawansa mulki, ‘ya’yan shugaba Bola Tinubu da na wasu manyan ‘yan siyasa suka fara kare manufofinsu duk da samun hadimani kan yaɗa labarai
- Seyi Tinubu da Folashade Tinubu-Ojo sun fito fili suna kare uban nasu yayin da ‘ya’yan Nasir El-Rufai da Atiku Abubakar da sauransu suka shiga fafutukar siyasa
- Wannan mataki na ‘ya’yan ‘yan siyasa ya fara bayyana ne yayin da ake fara shirin zabukan 2027 da hada-hadar jam’iyyu da ‘yan takara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Bayan hawansa mulki a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu 2023, Bola Tinubu ya sauya tsarin siyasar Najeriya.
‘Ya’yansa da na wasu manyan ‘yan siyasa sun fara kare iyayensu a fili, duk da kuwa suna da hadimai kan yaɗa labarai da ke aiki.

Asali: Twitter
Yadda yaran ƴan siyasa ke kare iyayensu
Baya ga Tinubu, wasu daga cikin ‘yan siyasar da ‘ya’yansu ke kare su sun hada da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa ƴaƴan masu galihu sun fara daukar wannan mataki ne yayin da iyayensu ke shirin zaben 2027.
Wadanda aka lissafo sun hada da shugaba Tinubu, Nasir El-Rufai da Atiku Abubakar, inda ‘ya’yansu ke shiga fafutukar kare su.
An bayyana cewa makasudin hakan shi ne don cimma burin siyasa a zaben gaba, koda kuwa ba su da mukaman gwamnati.
1. Folashade Tinubu-Ojo:
Ƴar shugaban kasa kuma Iyaloja-Janar ta jihar Lagos, na ta kokarin kare sunan mahaifinta a kafafen sada zumunta.
Ta taba rokon ‘yan Najeriya da su ba shugaban lokaci, tana mai cewa matsalolin tattalin arziki ba na Najeriya kadai ba ne.
Ta ce akwai bukatar ci gaba da hakuri da fatan alheri, domin kalubalen tattalin arziki na duniya ne gaba daya.
2. Seyi Tinubu:
Ɗan shugaban kasar, ya fito fili yana kare gwamnatin mahaifinsa da suka suka jawo ka-ce-na-ce daga abokan adawa.
A kwanan nan, Seyi ya halarci taron matasa a Yola, inda ya ce mahaifinsa shi ne shugaban da ya fi kowanne a tarihin Najeriya.
Ya kara da cewa abokan adawar mahaifinsa suna kai hari a kansa da iyalinsa, duk da kuwa shirinsa na matasa ba na siyasa ba ne.

Asali: Twitter
3. Bashir da Bello El-Rufai:
Ƴaƴan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, su na cikin masu kare mahaifinsu daga sukar ‘yan adawa.
Bello na wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a Majalisar Wakilai, yayin da Bashir ke amfani da kafafen sada zumunta don kare uban nasu.
Dukansu biyu sun kasance cikin manyan ‘ya’ya masu fada a ji a siyasar Arewa bayan saukar El-Rufai daga mulki.

Asali: Twitter
4. Shamsudeen Bala Mohammed:
Babban ɗa ga gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sha fitowa yana kare masu rigima da mahaifinsa musamman a kan siyasa.
A kwanakin nan ya zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da makircin siyasa a zaben 2023.
Ya kuma goyi bayan jita-jitar cewa mataimakin gwamnan Bauchi ya mari ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar.
Shamsudeen ya bayyana cewa siyasar Bauchi na cike da shisshigi da karan-tsaye daga abokan hamayya, Punch ta ruwaito.

Asali: Facebook
5. Mohammed Atiku:
Ɗan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, shi ne ya mayar da martani kan zargin da Shamsudeen Bala ya yi wa mahaifinsa.
Mohammed Atiku shi ne shugaban kungiyar goyon bayan Atiku (ASO), kuma ya kira kalaman Shamsudeen da girman kai da rashin mutunci.
Ya ce gwamnan Bauchi bai taba goyon bayan Atiku ba a tarihi, kuma yana ci gaba da aiki da masu adawa da shi, cewar wani rahoto a TheCable.
6. Adam Tuggar:
Adam Tuggar ya kasance ɗa ga ministan harkokin wajen Najeriya da ya fito daga jihar Bauchi.
Adam ya kalubalanci Shamsudeen Bala kan batun cewa an mari mahaifinsa da hannu yayin ziyara a Bauchi.
Ya ce kalaman dan gwamnan Bauchi karya ne kuma abin kunya, inda ya ce hakan ne ya sa dole ya fara tsoma baki a harkokin siyasa a kafafen sada zumunta.

Asali: Twitter
Illolin sauya shekar 'yan siyasa a Najeriya
Mun kawo muku rahoton yadda yawan sauya sheka ke yi tasiri a siyasar Najeriya duba da yadda zabe ya gabato.
Masana sun yi magana kan yawan samun sauya sheka a yanzu wanda suka ce zai yi tasiri a zaɓe da kuma dimukraɗiyya.
Hakan ya biyo bayan sauye-sauyen jam'iyyu da ake samu musamman a wannan karo daga jam'iyyun adawa zuwa APC.
Asali: Legit.ng